Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Kwalejin Koyon Aikin Lafiya ta MK College of Health Sciences da ke Kano ta rantsar da ɗalibanta 84 na farko, bayan samun amincewar hukumomin kula da ilimin lafiya da tabbatar da inganci.
Shugaban Sashen Koyar da Lafiya na kwalejin, Malam Mudassir Umar Farouk, ya bayyana hakan ne a yayin bikin yaye daliban da aka gudanar a Jami’ar Ilimi ta Yusuf Maitama Sule da ke Kano.
Ya ce kafin buɗe kwalejin, sun bi dukkan ƙa’idoji da sharuddan da doka ta tanada daga hukumomin lafiya na jiha da ƙasa. Ya ƙara da cewa makarantar na da ƙwararrun malamai da wadatattun kayan aiki, abin da ya taimaka wajen samar da dalibai masu ƙwarewa da fahimta.
Mudassir Umar Farouk ya jaddada cewa makarantar na koyar da darussa daban-daban da suka shafi kiwon lafiya, tare da haɗa ka’idojin aiki da kuma darussan da suka dace da addini da kyawawan al’adun al’umma.
Ya kuma yabawa hukumomi da cibiyoyin lafiya bisa haɗin kai da suke bai wa kwalejin, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage ƙarancin ma’aikatan lafiya da ake fama da shi.
