
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jami’an tsaro a Abuja, sun yi cincirindo a dukkan manyan titina da ke sassan Babban Birnin a wani yunƙuri na tabbatar da bin dokar taƙaice zirga-zirga yayin gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi a yau Asabar.
Wakilin Blueprint.ng da ya garzaya ta babban titin yankin Kubwa a Army Resource Centre da ke Asokoro ya bayyana yadda aka samu wasu masu taurin kai suka bijire wa dokar, inda dakarun soji suka dakatar da su.
A yayin haka ne aka hukunta su ta hanyar sanya su zama a ƙasa na tsawon sa’o’i tare faka motocinsu a gefe yayin da aka bar masu ayyuka na musamman suka cigaba da zirga-zirga bayan tantance su.
Kamar haka ya faru a yankin kasuwar Dutse, inda sojoji suka kori masu ƙoƙarin taka dokar.
An ga yadda jami’an tsaro ciki har ‘yan bijilante suka cika a hanyar da ke yankin Tipper Garage tare da zuba itatuwa waje rufe hanyar.
