Zidane ya amince wa zama kocin Faransa bayan Gasar Kofin Duniya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa, Zidane Zidane ya cimma yarjejeniyar baka domin zama sabon kocin Faransa bayan kammala Gasar Kofin Duniya na 2026.

A halin yanzu dai, tawagar Faransa na ƙarƙashin jagorancin Didier Deschamps, inda suna mayar da hankali kacokan akan gasar.

Ana sa ran bayan an kammala, Zidane zai karɓi ragamar yayin da ya dawo kan kujerar horarwa, kamar yadda ƙwararren ɗan jaridar wasanni Fabrizio Romano ya ruwaito.

Wannan shi ne karo na farko da Zidane ya karɓi aikin horarwa tun bayan barin sa Real Madrid a shekarar 2021, wanda a lokacin zamansa a can ya taimaka wa ƙungiyar nasarar lashe kofin Champions League har sau uku a jere.

By Babaji