Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ɗan majalisar wakilai, mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Ƙaura Namoda da Birnin Magaji, a Jihar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya raba buhunan hatsi iri-iri har 52,000 ga mazauna Jihar Zamfara domin rage wahalhalun tattalin arziki a lokacin azumin Watan Ramadana da muke ciki.
Da ya ke jawabi a wajen ƙaddamar da rabon a Gusau yau Asabar, Hon. Sani Jaji ya ce, hatsi iri-iri da ya bai wa mutane sun ƙunshi buhunan gero, masara, dawa da shinkafa.
Hakazalika ya bayyana cewar waɗanda za su amfana da tallafin sun haɗa da marayu, ‘yan gudun hijira, mata marasa galihu, ‘yan Jam’iyyar APC, mutanen da ke da buƙatu na musamman, matasa, da malaman Musulunci.
Ya ce tallafin ya shafi dukkan ƙananan hukumomi 14 a Jihar Zamfara.
Hon. Jaji ya buƙaci kwamitin rarraba hatsin da su tabbatar da adalci, kuma ya buƙaci waɗanda su ka amfana da tallafin da su yi amfani da tallafin yadda ya kamata.
“Wannan tallafin ba na sayarwa bane kuma na mutane ne a faɗin ƙananan hukumomi 14 na Zamfara, ba na mazaɓata kaɗai ba.” – Hon. Aminu Sani Jaji ya ce.
Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni a jihar da suyi amfani da lokacin azumin Watan Ramadana domin taimaka wa marasa galihu domin su aiwatar da azumin cikin sauƙi.
“Ina so in yi kira ga kowa da kowa musamman mawadata da su yi amfani da dukiyar su ta hanyar taimaka wa mutane masu rauni musamman a wannan lokacin na Azumin Watan Ramadana domin su sami damar yin azumin cikin sauƙi”. Hon. Jaji ya ce
