Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wannan kuwa ya faru ne a wani samame na haɗin gwiwar jami’an tsaro da aka kai a Tuddan Dargaza da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa.
Aikin na sirri ya samu jagoranci daga hukumar DSS tare da haɗin gwiwar sojoji ’yan sanda da kuma Community Watch Corps, lamarin da ya kai ga kama mutane huɗu da ake zargi, waɗanda a yanzu haka ake ci gaba da bincike a kansu.
Waɗanda aka ceto sun haɗa da mata 16, maza biyu da jarirai uku, waɗanda aka yi garkuwa da su daga Kauyen Gidan Sarkin Bayero a ƙaramar hukumar Musawa da sauran wurare.
Cikin waɗanda aka ceto, 20 kiristoci ne yayin da biyu musulmai ne, abin da ke nuna cewa ta’addancin ’yan bindiga ba ya la’akari da addini, tare da nuna ƙudurin gwamnati na kare dukkan al’umma ba tare da bambanci ba.
Aikin ya fi mayar da hankali ne kan maɓoyar fitaccen shugaban ’yan bindiga Kamilu Chiroma wanda aka fi sani da Buzaru, a Tuddan Dargaza.
Wannan nasarar ta nuna ingancin ayyukan tsaro na sirri da kuma haɗin kan hukumomin tsaro.
Gwamnatin jihar ta bakin kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Danmusa ta tabbatar wa da jama’a cewa waɗanda ake zargi za su fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada bayan kammala bincike.
Dr Nasiru Ɗanmusa ya jaddada ƙudurin Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa na kawo ƙarshen ’yan bindiga da maido da zaman lafiya a faɗin Jihar Katsina.
Ya yaba da kwarewar da jarumtakar DSS, sojoji, ’yan sanda da Community Watch Corps a yayin aikin.
