Uwargidan Gwamnan Zamfara ta ƙaddamar da raba tallafin azumi

Spread the love

Gaga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta ƙaddamar da shirin raba tallafin azumin watan Ramadana da bukukuwan Sallah a faɗin jihar a ranar Asabar, wanda hukumar zakkat da waƙafi ta samar.

Shirin ya mayar da hankali ne kan marayu 16,000 da marasa galihu a faɗin majalisun masarautu 19 na jihar.

Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta bayyana cewa an tantance waɗanda suka ci gajiyar shirin kuma za a ba su buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 25, tallafin kuɗi ₦20,000, kayan sutura ga kowanne.

“Muna ƙaunarku, muna ɗaukar ku da daraja, za a cigaba da kula daku a wannan tafiyar, Kuma zamu kasance tare da ku, muna goyon bayanku” Uwargidan Gwamnan ta ce.

Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta ƙara da cewa shirin raba tallafin yana da nufin haɓaka mutunci da dogaro da kai ga waɗanda suka ci gajiyar shirin.

“Shirin yana nuna jajircewar gwamnati na inganta jin daɗin ‘yan ƙasa marasa galihu, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal.” Ta bayyana

A cewar ta, gwamnatin jihar kwanan nan ta ɗauki nauyin auren marayu mata 200 (₦200,000 sadaki ga kowanne), biyan basussukan da suka shafi bashi, tallafin kasuwanci ₦50,000 ga ‘yan kasuwa 200, horar da kiwon kaji da kuma horar da ilimin kwamfuta ga marayu 10.

Uwargidan Gwamnan ta yaba wa hukumar zakka da wakafi ta Jihar da masu ruwa da tsaki kan sadaukarwar da suka yi.

By ukarofi