An yaba wa matan ƙaramar Hukumar Bichi bisa nuna ƙwazo a harkar sana’o’i

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An yaba wa matan ƙaramar Hukumar Bichi bisa jajircewa da haɗin kan da suke nunawa wajen koyon sana’o’in dogaro da kai domin inganta rayuwarsu da ta iyalansu.

Daraktan Mulki na ƙaramar Hukumar Bichi, Alhaji Abba Muhammad ɗiso, ne ya bayyana hakan yayin da ƙaramar hukumar ta karɓi baƙuncin Mai Bai wa Gwamnan Jihar Kano Shawara kan Ayyukan Gayya da Sa-kai, Alhaji Isma’il Shehu Gurjiya.

Alhaji Abba Muhammad ɗiso ya jaddada cewa matan yankin na da burin inganta zamantakewar aure da tarbiyyar yara, kasancewar su ne ginshiƙan iyali da al’umma. Ya kuma yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa ƙoƙarin da take yi wajen tallafa wa shirye-shiryen da ke taimaka wa rayuwar jama’a.

“An yi gwamnoni da dama a Kano, amma kowa ya san yadda ake gudanar da ayyuka a yanzu akwai bambanci. Muna godiya da irin waɗannan ayyukan alheri da kuma yadda Gwamna ke zaɓar mutanen da suka dace da aiki,” inji shi.

Shi ma da yake jawabi, Alhaji Isma’il Shehu Gurjiya ya bayyana cewa manufar Gwamna Abba Kabir Yusuf ita ce tallafa wa duk wanda ke da burin taimaka wa kansa da al’umma gaba ɗaya.

“Gwamnatin Kano na da burin tallafa wa masu himma da ƙwazo. Mun zo ne domin mu saurari buƙatunku, mu tattara bayanai mu miƙa wa Mai Girma Gwamna domin a duba irin gudunmawar da za a bai wa ƙungiyoyin Aikin Gayya da Sa-kai wajen haɓaka rayuwa da tattalin arziki,” inji Gurjiya.

A nasu ɓangaren, Shugaban ƙungiyar Aikin Gayya ta ƙaramar Hukumar Bichi, Malam Garba Tsoho, tare da Ma’ajin ƙungiyar, Malam Yusuf Tambai ɗansiri, sun gode da ziyarar tare da bayyana wasu ƙalubale da suke fuskanta.

Sun ce daina bayar da alawus na kwamitoci da kuma rashin kayan aiki kamar shebur, diga da sauran su na daga cikin abubuwan da suka janyo koma baya ga ayyukan gayya a yankin. Sun buƙaci a dawo da irin waɗannan tallafi domin farfaɗo da ayyukan tsaftace muhalli da ci gaban al’umma.

“Muddin aka samar da waɗannan kayan aiki da tallafi, za a samu cigaba sosai. Mu a shirye muke ko da dare ko rana mu fito mu gyara duk wurin da ake buƙatar tsaftacewa,” inji Malam Garba Tsoho.

Haka kuma, shugabannin ƙungiyoyin bunƙasa sana’o’in mata, ciki har da Malama Rakiya Abdullahi Bichi, sun roƙi gwamnatin jiha da ta tallafa musu da kayan koyon sana’o’i kamar kekunan ɗinki, injinan saƙa, kayan kiwon kaji da kuma tallafin noma na rani da damina domin ƙarfafa mata su dogara da kansu.

Ziyarar ta kasance wata dama ta tattaunawa tsakanin gwamnati da al’umma kan hanyoyin farfaɗo da ayyukan gayya da kuma ƙarfafa sana’o’in mata a Ƙaramar Hukumar Bichi.Yadda matan ƙaramar Hukumar Bichi suka nuna ƙwazo a harkar sana’o’i

An yaba wa matan ƙaramar Hukumar Bichi bisa jajircewa da haɗin kan da suke nunawa wajen koyon sana’o’in dogaro da kai domin inganta rayuwarsu da ta iyalansu.

Daraktan Mulki na ƙaramar Hukumar Bichi, Alhaji Abba Muhammad ɗiso, ne ya bayyana hakan yayin da ƙaramar hukumar ta karɓi baƙuncin Mai Bai wa Gwamnan Jihar Kano Shawara kan Ayyukan Gayya da Sa-kai, Alhaji Isma’il Shehu Gurjiya.

Alhaji Abba Muhammad ɗiso ya jaddada cewa matan yankin na da burin inganta zamantakewar aure da tarbiyyar yara, kasancewar su ne ginshiƙan iyali da al’umma. Ya kuma yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa ƙoƙarin da take yi wajen tallafa wa shirye-shiryen da ke taimaka wa rayuwar jama’a.

“An yi gwamnoni da dama a Kano, amma kowa ya san yadda ake gudanar da ayyuka a yanzu akwai bambanci. Muna godiya da irin waɗannan ayyukan alheri da kuma yadda Gwamna ke zaɓar mutanen da suka dace da aiki,” inji shi.

Shi ma da yake jawabi, Alhaji Isma’il Shehu Gurjiya ya bayyana cewa manufar Gwamna Abba Kabir Yusuf ita ce tallafa wa duk wanda ke da burin taimaka wa kansa da al’umma gaba ɗaya.

“Gwamnatin Kano na da burin tallafa wa masu himma da ƙwazo. Mun zo ne domin mu saurari buƙatunku, mu tattara bayanai mu miƙa wa Mai Girma Gwamna domin a duba irin gudunmawar da za a bai wa ƙungiyoyin Aikin Gayya da Sa-kai wajen haɓaka rayuwa da tattalin arziki,” inji Gurjiya.

A nasu ɓangaren, Shugaban ƙungiyar Aikin Gayya ta ƙaramar Hukumar Bichi, Malam Garba Tsoho, tare da Ma’ajin ƙungiyar, Malam Yusuf Tambai ɗansiri, sun gode da ziyarar tare da bayyana wasu ƙalubale da suke fuskanta.

Sun ce daina bayar da alawus na kwamitoci da kuma rashin kayan aiki kamar shebur, diga da sauran su na daga cikin abubuwan da suka janyo koma baya ga ayyukan gayya a yankin. Sun buƙaci a dawo da irin waɗannan tallafi domin farfaɗo da ayyukan tsaftace muhalli da cigaban al’umma.

“Muddin aka samar da waɗannan kayan aiki da tallafi, za a samu cigaba sosai. Mu a shirye muke ko da dare ko rana mu fito mu gyara duk wurin da ake buƙatar tsaftacewa,” inji Malam Garba Tsoho.

Haka kuma, shugabannin ƙungiyoyin bunƙasa sana’o’in mata, ciki har da Malama Rakiya Abdullahi Bichi, sun roƙi gwamnatin jiha da ta tallafa musu da kayan koyon sana’o’i kamar kekunan ɗinki, injinan saƙa, kayan kiwon kaji da kuma tallafin noma na rani da damina domin ƙarfafa mata su dogara da kansu.

Ziyarar ta kasance wata dama ta tattaunawa tsakanin gwamnati da al’umma kan hanyoyin farfaɗo da ayyukan gayya da kuma ƙarfafa sana’o’in mata a ƙaramar Hukumar Bichi.

By ukarofi