Gwamnatin Katsina ta rage lokutan aikin ma’aikata saboda Ramadan

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da rage lokutan aikin ma’aikatan gwamnati domin ba su damar gudanar da ibada cikin sauƙi a watan azumin Ramadan.

Sanarwar ta fito ne daga ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin Jihar, inda sanarwar ta bayyana cewa gwamnan jihar, Dikko Umaru Raɗɗa, ya amince da sauyin domin bai wa ma’aikata damar halartar karatun tafsir da sauran ayyukan ibada a wannan wata mai albarka.

A cewar sanarwar, sabon tsarin ya fara aiki daga ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026. Ƙarqashin tsarin, ma’aikata za su riƙa aiki daga ƙarfe 7:30 na safe zuwa 2:30 na rana daga Litinin zuwa Alhamis, yayin da a ranar Juma’a za a tashi da ƙarfe 12:00 na rana.

Gwamnatin ta umarci dukkan ma’aikatun gwamnati, sassa da hukumomi (MDAs) da su tabbatar da cikakken bin wannan tsari ba tare da tangarɗa ba, tare da ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.

Sanarwar, wadda Jafaru Abdullahi Maikaje ya sanya wa hannu a madadin shugaban ma’aikatan gwamnatin Jihar, ta buƙaci ma’aikata da su yi aiki da sabon tsarin tare da kiyaye ƙa’idojin aiki.

Rage lokutan aiki a watan Ramadan na daga cikin matakan da wasu jihohi ke ɗauka domin sauƙaƙa wa ma’aikata yayin azumi, tare da tabbatar da cewa harkokin gwamnati na tafiya yadda ya dace.

By ukarofi