Ramadan: Jabiru Tsauri ya raba tallafin Azumi na Naira Miliyan 300 a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban AUDA-NEPAD, Alhaji Jabiru Tsauri (Lamiɗon Katsina), ya ƙaddamar da rabon tallafin Azumi na kimanin Naira miliyan 300 ga al’ummar shiyyar Katsina da wasu sassan Jihar Katsina.

An ƙaddamar da shirin rabon tallafin ne a gidansa da ke cikin garin Katsina, inda al’umma suka ci gaba da zuwa domin karɓar nasu kason na kayayyaki da kuma kuɗin cefane.

Tallafin ya haɗa da kayan abinci irinsu shinkafa, sukari da gero, tare da kuɗin cefane domin tallafa wa masu amfana rage raɗaɗin tsadar rayuwa a wannan wata mai alfarma.

Waɗanda suka amfana da tallafin sun haɗa da malamai, limamai, shugabannin jam’iyyun siyasa, masu ruwa da tsaki a ƙananan hukumomi, da kuma wakilan ƙungiyoyi daban-daban.

Haka kuma gidajen marayu da na gajiyayyu, ƙungiyoyin siyasa, na al’umma, na matasa, na mawaƙa da kuma ƙungiyoyin marubuta a kafafen sada zumunta sun samu rabon tallafin.

A rana ta farko ta rabon, ƙananan hukumomi shida ne suka fara karɓar tallafin, ciki har da Safana, Ɗanmusa, Ɓatagarawa, Rimi, Katsina da Dutsinma.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da shirin, Alhaji Jabiru Tsauri ya bayyana cewa tallafin na daga cikin ayyukan jin ƙai da yake gudanarwa lokaci zuwa lokaci domin tallafa wa al’umma, musamman a watan Ramadan. Ya ƙara da cewa baya ga wannan shiri, yana da wasu tsare-tsare na tallafa wa marasa lafiya, ɓangaren ilimi da sauran fannoni na rayuwar al’umma.

Wasu daga cikin waɗanda suka amfana sun bayyana jin daɗinsu kan tallafin, inda suka ce hakan zai taimaka musu wajen sauƙaƙa musu gudanar da ibadun watan Azumi cikin kwanciyar hankali.

By ukarofi