Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na wannan makon. Sannunku da jimirin bibiyarmu.
A wannan satin da yardar mai kowa mai komai za mu kai ƙarshen wannan darasin da ya ɗauke mu tsawon sati huɗu.
8. Goge matattun ƙwayoyin fata cikin hikima:
Akwai hanyar da ake bi wurin goge fata ta amfani da wasu amintattun kayan goge matattar fata cikin sauƙi. Saidai yana da kyau matuƙa lura da irin kayan da ya kamata a yi amfani da su. Za a goge a hankali sau ɗaya zuwa uku a mako (ya danganta da irin ƙarfin fatar mutum) domin cire matattun ƙwayoyin fata da buɗe hanya ga sabuwar fata. A guji goge-goge mai tsanani da ke iya haddasa kaikayi da kumburi.
9. Guje wa taɓa wa ko matse kuraje:
ɗaya daga cikin ɗabi’un da muke ganin kamar zai haifa mana ɗa mai ido a gyaran fata shi ne ƙoƙarin kawar da ƙurji ta ƙarfin tuwo. Saidai abinda ba mu sani ba, matse kuraje na iya haddasa kumburi, kamuwa da ƙwayoyin cuta, da barin tabo mai wuyar tafiya. Maimakon haka, za a iya amfani da kayan kawar da ƙuraje wanda zai kashe su a hankali, kuma ya ba wa fata damar warkewa a hankali.
10. Wanke abubuwan da ke tu’ammali da fuska akai-akai:
A riƙa wanka kayan shafe-shafe, filo, da kuma tsaftace wayoyin hannu domin kawar da ƙwayoyin cuta da ke iya haddasa matsalolin fata.
