Daga SA’ADATU SAMINU KANKIA
Ba wai kawai a wannan watan ake buƙatar ma’aurata su zama masu mu’amala mai kyau a tsakaninsu ba, a kullum, a kodayaushe ana buƙatar ganin cewa ma’aurata sun zama masu tafiyar da rayuwarsu ta zamantakewar aure cikin fahimta, mutuntawa da ganin girma da darajar junansu.
Da yake wannan watan wata ne mai yawan darajoji da kuma albarka, yana da kyau musamman ga ma’auratan da ba su da ɗabi’ar daraja junansu da su yi amfani da wannan rubutu domin gyara zamantakewar zamansu na aure da niyar ci gaba da kyawawan ɗabi’un daga wannan lokaci har ya zuwa ƙarshen rayuwarsu ta zaman aurensu.
A kullum, musamman a wannan watan duk wata mace tana sha’awar ganin cewa mijinta ya ciyar da su daɗaɗan abinci, abin sha da kayan marmari na halas.
Haka suma maza a kowanne irin yanayin da suka samu kansu na akwai ko babu, fatansu shine su ga cewa sun ciyar da iyalansu duk wani abu mai daɗi musamman ma a wannan watan, inda za a ga yadda magidanta maza suke ƙoƙarin tanadarwa iyalansu duk wasu abubuwa na marmari da mai azumi zai yi sha’awa kamin shan ruwa da kuma bayan shan ruwa. Sai dai akasarin maza babu abinda suke kokawa da shi sai yadda wasu matan suke wulaƙanta kayan abinci da abubuwan da aka tanadar musu musamman a wannan watan.
Ba ma wulaƙanta kayan da almubazzaranci da matan ke yiwa kayan abincin ba, wani baƙar ɗabi’ar ko al’ada da wasu matan ke da shi shine, a lokacin da aka shigo musu da kayan abinci ko na azumi, ba su da lokacin da zasu daga kai su kalli kayan ma barema su kawar da su, ko su bada umurinin ɗaukesu domin adanasu a inda ya kamata, wannan wata mummunar ɗabi’a ce da akasarin maza suke kokawa da ita.
Yana daga cikin kyakkyawar mu’amala ta zamantakewar aure, a duk lokacin da miji ya shigo da kayan abinci ko ya aiko ayi gaggawar ɗaukesu a kuma adanasu a inda ya kamata. Idan ma kina da kishiyoyi aka baku wani abu domin raba wa a tsakaninku, ko kuma ko wacce an bata nata, duk wadda tayi saurin adana nata ita zata fi burge maigidan, kuma har a cikin zuciyarshi zaya ji daɗi, saboda ta mutuntashi kuma ta nuna tasan darajar abinda ya kawo.
Ya ke ‘yar’uwa ki sani, adana duk abinda mai gida ya kawo wajibi ne akanki, kuma wannan abin da zakiyi zaya ƙara ɗaukaka darajarki, kuma za ya sanya ya ji daɗi gobe ma idan ya fita ya yi ƙoƙarin samowa ya kawo. Ba dole sai abinda ya kawo maku ba, kulawa da adana duk wani abu daya kawo wajibi ne akan duk wata mace dake son zaman aure.
Mata da dama suna ganin cewa ba dole ba ne su yiwa maigida godiya a lokacin da ya kawo wani abu da take ganin cewa haƙƙin sa ne, hakan kuma ba ƙaramin kuskure ba ne, ga duk macen da bata san ta cewa mijinta ta gode ba game da duk wani abu na dole ko na kyautatawa da ya yi mata, hakan ne zai sa gaba ba zai yi sha’awar ganin ya yi wani abin kyautatawa ba koda yana da niya da kuma sha’awar son yi. Yin godiya ga miji yana ƙara ma mace ƙima tare da sanya shi ya ji daɗi ganin ya yi wani abu da ya burgeki.
Da yake wannan watan wata ne da aka kwaɗaitar da al’ummar Musulmi yin alheri, nasan maza da dama suna ƙoƙarin ganin cewa sun kyautatawa matansu da duk wani na kusa da su, don haka duk ƙanƙantar kyauta mace ta yi godiya kuma ta nuna farin cikinta da ita.
