Tare da BILKISU YUSUF ALI
Bindoka ginshiƙi ce ta zaman lafiya, adalci da daidaito a kowace al’umma. Doka ita ce ke tsara rayuwar jama’a, tana fayyace haƙƙoƙi da nauye-nauyen mutane, tare da samar da tsarin hukunci ga masu karya doka. A duk inda bindoka ta tsaya ƙafafunta, al’umma kan samu kwanciyar hankali, ci gaba da walwala. A gefe guda kuma, inda aka yi watsi da bindoka, rikice-rikice, zalunci da koma bayan tattalin arziƙi kan yawaita. A tarihi da zamani, masana siyasa, shari’a da zamantakewa sun jaddada cewa ba za a iya gina al’umma ta gari ba sai an gina bindoka mai ƙarfi wadda kowa ke mutunta ta.
Ma’anar bin doka
Bin doka tana nufin tarin ƙa’idoji, dokoki da tsare-tsare da al’umma ko gwamnati ke shimfiɗawa domin tsara rayuwar jama’a, kare haƙƙoƙi, da tabbatar da adalci. Bin doka ba wai dokoki ne kawai da aka rubuta ba, har ma ta haɗa da ƙa’idojin al’ada da na addini da jama’a suka amince da su tsawon lokaci.
Masana shari’a suna kallon bin doka a matsayin yarjejeniya tsakanin jama’a da gwamnati, inda kowa ke amincewa da iyakoki da dokoki domin samun zaman lafiya. Bin doka tana da ikon hukunta masu karya doka tare da kare masu bin doka. A wannan ma’ana, bin doka ita ce tubalin gina tsari, doka da oda a kowace al’umma.
Bin doka na iya kasancewa ta rubuce (kamar kundin tsarin mulki da dokokin majalisa) ko kuma ta al’ada (dokokin gargajiya da na addini). Duk da bambancin nau’i, burin bin doka ɗaya ne: wato tabbatar da daidaito, tsaro da adalci a cikin al’umma.
Muhimmancin bin doka ga rayuwar al’umma
1. Samar da zaman lafiya da tsaro
Bin doka na hana aikata laifuka ta hanyar shimfiɗa hukunci ga masu laifi. Idan jama’a sun san akwai hukunci mai tsauri, hakan na rage aikata laifuka kamar sata, fashi da makami, garkuwa da mutane da rikice-rikice. Zaman lafiya da tsaro su ne ginshiƙan duk wani ci gaba.
2. Kare haƙƙoƙin ɗan’Adam
Bin doka na kare haƙƙin kowane ɗan ɗasa, komai matsayin sa. Ta tanadi dokoki da ke kare rayuwa, mutunci, dukiya, ’yancin faɗar albarkacin baki da addini. Wannan kariya na hana zalunci da danniya.
3. Samar da adalci da daidaito
Bin doka na tabbatar da cewa kowa da kowa ya yi daidai a gaban doka. Wannan ƙa’ida na hana fifiko ko nuna wariya, yana kuma ƙarfafa amincewa tsakanin jama’a da hukumomin shari’a.
4. Tsara rayuwar jama’a
Dokoki na tsara mu’amala a fannoni daban-daban kamar aure, gado, kasuwanci, aiki da siyasa. Wannan tsari na rage rikice-rikice da saɓani a cikin al’umma.
5. Gina mutunci da tarbiyya
Bin doka na koya wa jama’a ladabi, hakuri da mutunta juna. Al’umma mai bin doka tana haifar da ’ya’ya masu tarbiyya da nagarta.
Tasirin bin doka wajen gina al’umma ta gari
1.Gina nagartaccen mulki
Bin doka na tabbatar da cewa gwamnati tana aiki ne bisa doka, ba bisa son rai ba. A Nijeriya, kundin tsarin mulki ya tanadi rabuwar iko tsakanin bangarorin gwamnati (zartarwa, majalisa da shari’a), wanda hakan ke hana mulkin kama‑karya da zalunci.
2. Ci gaban tattalin arziki
ƙasashe da jihohin da ke da bin doka suna samun ci gaban tattalin arziki. A Arewacin Nijeriya, samar da dokokin kasuwanci da kare dukiyar jama’a ya taimaka wajen bunƙasar kasuwanni kamar Kantin Kwari (Kano) da kasuwannin shanu a jihohi daban‑daban.
3. Inganta tsaro da zaman lafiya
Aiwatar da dokokin tsaro da hukunta masu aikata laifi na taimakawa rage rikice‑rikice. Misali, kafa kotunan Shari’a da na gargajiya a Arewa ya taimaka wajen warware rikice‑rikice cikin lumana.
4. Inganta ilimi da tarbiyya
Dokokin da suka wajabta ilimin firamare da kare haƙƙin yara a Nijeriya sun taimaka wajen rage bautar da yara.
5. Rage rikice‑rikice da ƙarfafa haɗin kai
A al’ummar Hausawa, bin dokokin gargajiya da shari’ar Musulunci suna taka rawa wajen sasanta rikice‑rikicen aure, gado da ƙabilanci ba tare da tashin hankali ba.
Za mu cigaba a mako mai zuwa insha Allah
