Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jakadan ƙasar Saudiyya a Nijeriya, Yousef Albalawi, ya sanar da cewa kamfanin jiragen sama na Saudiyya zai dawo da zirga-zirga kai tsaye daga Jiddah zuwa Abuja nan da watan Yuni ko kuma a watan Janairun 2027.
Jakadan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, a Abuja.
A cewarsa, ziyarar na da nufin ƙara danƙon alaƙa tsakanin Saudiyya da Nijeriya tare da faɗaɗa damar haɗin gwiwa a fannoni daban-daban, musamman tattalin arziki, siyasa da tsaro.
Albalawi ya jaddada cewa Saudiyya za ta ci gaba da hidimtawa ’yan Nijeriya da ke son zuwa Umrah da Hajji, yana mai cewa ƙasarsa na bai wa alaƙar tarihi da kimar bai ɗaya da ke tsakanin ƙasashen biyu muhimmanci.
Ya kuma bayyana aniyarsa ta yin aiki tare da ma’aikatar da kafafen yaɗa labarai domin gyara duk wata fahimta mara kyau game da Saudiyya, tare da nuna ainihin hoton ƙasar.
Da yake mayar da martani, Minista Idris ya ce ziyarar ta nuna irin muhimmancin da ofishin jakadancin Saudiyya ke bai wa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, tare da ƙara tabbatar da kyakkyawar alaƙar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.
Ya ce Gwamnatin Tarayya na da niyyar zurfafa haɗin gwiwa da Saudiyya a ɓangarorin tattalin arziki, tsaro da sauran fannoni masu anfani ga al’umma.
Ministan ya bayyana cewa Nijeriya ta riga ta amince da wasu yarjejeniyoyi uku da Saudiyya ta gabatar. ɗaya daga cikinsu shi ne haɗin gwiwa kan musayar labarai tsakanin Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) da Saudi Press Agency.
Haka kuma akwai yarjejeniya ta biyu kan haɗin gwiwa a ɓangaren rediyo da talabijin tsakanin NTA da Hukumar Yaɗa Labaran Saudiyya.
Yarjejeniyar ta uku kuwa ta shafi haɗin gwiwa a ɓangaren kafafen yaɗa labarai na sauti da hoto tsakanin Hukumar Kula da Kafofin Sauti da Hoto ta Saudiyya da NBC.
Idris ya ƙara da cewa ana sa ran zai gana da takwaransa na Saudiyya domin ƙarfafa aiwatar da waɗannan yarjejeniyoyi, da nufin tabbatar da amfanin haɗin gwiwar ga ƙasashen biyu.
