Lakurawa sun halaka mutum shida a wajen tafsiri a Kebbi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Aƙalla masu ibada shida ne suka rasa rayukansu yayin da wasu suka jikkata sakamakon harin da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne suka kai kan wani masallaci a ƙauyen Dadinkowa da ke ƙaramar Hukumar Maiyama ta jihar Kebbi.

Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kewaye masallacin ne a lokacin da ake gudanar da zaman Tafsirin Alkur’ani da daddare, kafin su buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

An ce bayan harin, an fitar da gawawwakin mutum shida domin gudanar da sallar jana’iza, inda aka tabbatar da cewa shida ne suka mutu, kuma aka binne su bisa tsarin addinin Musulunci.

Wata mujalla mai bibiyar lamuran yaƙi da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi ta ruwaito cewa harin na iya kasancewa ramuwar gayya ne bayan wani shiri na kwanton ɓauna da sojoji suka daƙile a farkon makon nan. A cewar rahoton, maharan sun kai farmaki ne da yammacin Laraba yayin da jama’a ke cikin ibada, suna harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa.

Ana zargin harin ya biyo bayan wani samame da dakarun Operation FANSAN YANMA suka kai, inda suka hallaka mutane biyar da ake zargi ‘yan Lakurawa ne a kusa da tsaunin Mayama. An ce samamen ya biyo bayan yunƙurin kwanton ɓauna da aka yi wa ayarin motocin Babban Hafsan Runduna ta 8 yayin rangaɗin aiki a jihar.

A yayin artabun, sojoji sun kwato bindigu da harsasai da dama, ciki har da bindigar OJC, PKT, bindigogin AK-47 guda biyu, gidan harsasai huɗu na AK-47, alburusai masu nauyin 12.7mm, jakar kuɗi zauke da naira 840,000, wayoyin salula biyu da babura biyar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa harin ramuwar gayya ne bayan gaza kai hari ga dakarun runduna ta 8. Ya ce mutum biyar sun mutu nan take sakamakon harbin bindiga, yayin da wasu uku suka samu raunuka daban-daban, aka kai su asibiti domin jinya.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan yawaitar hare-haren Lakurawa a yankin Arewa maso Yamma. A ranar 20 ga Fabrairu ma, aƙƙlla mutane 33 ne suka mutu a jerin hare-hare da aka kai wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Arewa ta jihar Kebbi.

Harin masallacin ya sake jaddada aalubalen tsaro da ke addabar wasu sassan ƙasar, inda al’umma ke rayuwa cikin fargaba da rashin tabbas, duk da ƙoƙarin jami’an tsaro na daaile barazanar ’yan ta’adda.

By ukarofi