An gudanar da addu’o’i da karatun Alƙur’ani bisa cika shekara ɗaya da rasuwar Garkuwan Legas

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

An gudanar da taron addu’o’i da karatun Alƙur’ani mai girma domin tunawa da cika shekara ɗaya da rasuwar Garkuwan Legas kuma Sarkin Bai na Jihohi goma sha bakwai na Kudancin Nijeriya, Alhaji Shehu Rabiu ‘Yar Musa, a ranar Lahadi.

An yi taron ne a Fadar Sarkin Hausa Layi da ke unguwar Ajegunle a Jihar Legas, inda ya samu halartar jama’a da dama daga ciki da wajen Legas, ciki har da malamai, sarakunan gargajiya, ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ‘yan uwa da abokan arziki.

Alhaji Musa Shehu ‘Yar Musa, ɗan marigayin wanda yanzu shi ne magajinsa, ya miƙa godiyarsa ga duk waɗanda suka halarci taron addu’a da karatun Alƙur’ani da aka gudanar domin mahaifinsa.

“Ina yi wa dukkan jama’ar da suka halarci wannan taro na yau godiya tare da yi musu fatan alheri. Ganin yadda mutane daga wurare daban-daban suka zo domin halartar taron addu’a ga mahaifina ya nuna cewa ya zauna da mutane cikin zaman lafiya a lokacin rayuwarsa,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Arewa mazauna Legas da sauran sassan ƙasa da su zauna lafiya da juna ba tare da nuna ƙiyayya ko haushin juna ba, tare da fatan mahalarta taron sun koma gidajensu lafiya.

A nasa ɓangaren, Alhaji Sule ɗanmaliki na Fadar Garkuwa ya gode wa jama’ar da suka halarci taron, yana mai yi musu addu’ar Allah Ya saka musu da alheri. Ya kuma roƙi Allah Ya kyautata makwancin marigayin.

ɗanmalikin ya yi kira na musamman ga matasa, yana mai cewa su ne ƙashin bayan kowace al’umma a fannoni daban-daban na rayuwa da suka haɗa da tattalin arziƙi, kasuwanci, aikin gwamnati da siyasa.

“Saboda haka ina kira ga matasa da su tashi tsaye wajen neman ilimi da sana’o’i, tare da guje wa shaye-shaye domin kuwa idan matasa suka lalace, al’umma ma za ta lalace,” in ji shi.

Haka kuma ya buƙaci al’umma da su yi amfani da watan Azumi wajen yi wa ƙasar Nijeriya addu’ar samun ɗorewar zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziƙi.

Taron ya samu halartar jama’a masu yawa, inda mahalarta suka rika bayyana irin kyawawan halaye da zaman lafiya da marigayi Garkuwan Legas ya yi da al’umma a lokacin rayuwarsa, tare da yaba masa kan kyautata wa jama’a da kuma haɗa kan al’umma.

By ukarofi