Daga AISHA ASAS
A ranar Alhamis, 19 ga watan Fabrairu, 2026, duniya ta yi rashin Eric Dane, ɗan wasan kwaikwayo da ya shahara sosai musamman a rawar da ya taka a cikin shahararren shirin talabijin na likitanci mai suna Grey’s Anatomy, inda ya yi fice a matsayin Dr. Mark Sloan, wanda masoya suka fi sani da laƙabin McSteamy. Dane ya rasu yana da shekaru 53, bayan doguwar gwagwarmaya da cutar amyotrophic lateral sclerosis (ALS), wadda aka fi sani da Lou Gehrig’s disease, cuta mai haddasa lalacewar jijiyoyin da ke sarrafa tsokoki kuma ba ta da magani a likitance.
Dane ya sanar da duniya cewa yana ɗauke da cutar ALS a watan Afrilu 2025, yana mai bayyana cewa wannan cuta ce mai tsanani wadda ke rage aikin jijiyoyin jiki tsawon lokaci. Cutar ta sa ya fara rasa ikon amfani da wasu gaɓoɓinsa, har ya kai ga amfani da kujera ta guragu. Duk da haka, ya ci gaba da fata da ƙoƙarin ganin ya yi tasiri sosai wajen wayar da kan jama’a kan cutar, har ya zama mai fafutukar tallata bincike da taimako ga wasu masu fama da cutar.
Dane ya kasance yana samun kulawa ta musamman daga iyalinsa a lokutan ƙarshe na rayuwarsa. Matarsa, Rebecca Gayheart, wacce ita ma fitacciyar ‘yar fim ce, da ‘ya’yansa biyu Billie da Georgia, waɗanda suka kasance garkuwa gare shi har ƙarshe rayuwarsa.
Dane ya kafa tarihi a duniyar talabijin bayan ya shiga cikin shirin ‘Grey’s Anatomy’ tun 2006 a matsayin Dr. Mark Sloan, likitan fata mai fasaha kuma wanda aka fi sani da McSteamy a tsakanin masoyansa. Wannan rawar ta sa shi zama ɗaya daga cikin taurarin da suka fi jan hankali a fagen wasan kwaikwayo na kimiyya da labarin rayuwa. A cikin shirin wanda yake mai dogon zango, Sloan ya yi fice ba kawai saboda kyan hali ba, har ma saboda haɗin kansa da wasu manyan jarumai waɗanda ke nuna ƙauna da rikice‑rikicen zamantakewa da suka shafi rayuwar likitoci da marasa lafiya a asibiti. Hakazalika rawar tasa ta kasance mai abin ban dariya tare da haushi a wurin wasu, wanda hakan ya sa a farkon fitowarsa ake masa kallon mayaudari ko wanda bai san ciwon kansa ba. Saidai duk da haka rawar tasa na birge masu kallo har da waɗanda ke jin haushin sa. Saidai daga baya jarumin ya fitar da asalin halin Dr. Mark Sloan wanda hakan ke nuna irin ƙwarewar da yake da ita.
Bayan barinsa ‘Grey’s Anatomy’, abin dariya da tausayi ya ci gaba da bayyana yayin da yake taka rawar gani a cikin sauran fina‑finai da jerin shirye‑shirye, ciki har da ‘Euphoria’, inda ya sake nuna ƙwarewa a matsayin Cal Jacobs, labari mai rikitarwa da kyan kallo.
A cikin shekarar 2025, yayin da cutar ALS ta ƙara tsananta masa, Dane ya zama mai magana kan rayuwa da ƙoƙarin mutane masu fama da irin wannan cuta. Ya yi kira ga jama’a da su fahimci cutar, su taimaka wajen neman magani da goyon baya ga masu fama da ita, da kuma ƙarfafa ƙungiyoyi masu gudanar da bincike. Ta wannan hanyar, ya ɗauki rawar jagoranci wajen bayar da haske kan irin wahalar da masu cutar ALS ke fuskanta.
A cikin wata hira ta musamman da aka saki bayan mutuwarsa, wadda wasu da dama suka bayyana ta a matsayin saƙon wasiya da ya bari, Dane ya yi amfani da damar don barin saƙonnin ƙarshe ga ‘ya’yansa matasan ‘yan mata biyu, inda ya bayyana soyayya marar misaltuwa da fatan da yake da shi cewa za su tsayu da ƙarfi a rayuwa: “Billie da Georgia, ku ne zuciyata, ku ne komai gare ni… Ina ƙaunanku.” Wannan ya kasance daga cikin ƙarshen saƙonninsa kafin ya bar duniya.
Wannan rashin ya jefa duniya cikin damuwa musamman tsakanin masoyan ‘Grey’s Anatomy’, inda mabiya shirin suka yi ta nuna alhini da tuna rawar da Sloan ya taka wajen ƙayatar da miliyoyin masu kallo.
ƙungiyar shirye‑shirye da abokan aikinsa ciki har da wasu daga cikin tsofaffin jarumai sun yi ta nuna girmamawa ga gudunmawar da ya bayar da kuma tsayin daka da jarumtakar da ya nuna har zuwa ƙarshe.
Duk da cewa tuni jarumi Dr. Mark Sloan ya mutu a cikin shirin ‘Grey’s Anatomy’ bayan haɗarin jirgi da ya faru da shi da wani likita a wani zango a baya, hakan bai hana mutuwar Dane a gaske ta haifar da ruɗani da baƙin ciki ga masoyansa na duniya baki ɗaya ba, saboda ya kasance jarumi mai armashi da ƙwarewa.
Yanayin yadda abokansa na cikin shirin mai dogon zango na ‘Grey’s Anatomy’ suka bayyana damuwa tare da alhini a kafafen sada zumunta kuwa sai ya mantar da mutane rashin sa a shirin na tsayin lokaci, domin sun bazama wallafa hotunansa tare da su a shirin, yayin da suke rubutu mai taɓa zuciya.
Da yawa daga cikin jaruman sun nuna masa hallaci bayan mutuwa ta hanyar bada gudunmawa mai tsoka ga iyalansa, wasu kuwa ga cibiyar da ke bincike kan cutar ALS wadda ta yi sanadiyar mutuwar sa.
Rashin Eric Dane a shekaru 53 bayan gwagwarmayarsa da cutar ALS babban rauni ne ga masana’antar nishaɗi ta Hollywood da masu kallon fina-finan Turanci na duniya baki ɗaya. Ya kasance ɗan wasa mai ban sha’awa, ya nuna ƙwarewa a mabambantan rawa da ya taka a fina-finai, da kuma rawar da ya taka wurin jagorancin ɗaga wayar da kan jama’a kan cutar da ke tattare da rayuwar miliyoyi, a daidai lokacin da yake fama da matsanancin ciwo da cutar ta haddasa masa.
Mutuwarsa ta bar gurbi mai wuyar cikewa, darasi, da burin ganin ci gaban bincike kan ALS da ƙarin tallafi ga waɗanda cutar ta shafa.
Ba za a taɓa mantawa da Eric Dane a matsayin McSteamy ba, da kuma a matsayin mutum mai ƙoƙari da zuciya mai tausayawa.
