Daga WAKILINMU
An sake yaba wa gidauniyar Hazras Charity Foundation bisa yadda take gudanar da shirye-shiryen tallafa wa al’umma marasa ƙarfi, inda aka buƙaci sauran ƙungiyoyi su yi koyi da tsarinta da tsarin aikinta wajen kai agaji ga mabuƙata.
Gidauniyar, wadda ke aiki ƙarƙashin jagorancin Muslims Aid Australia (MAA), ta raba kayan abinci na azumi ga zaɓaɓɓun al’umma a jihohin Neja, Kano da Yobe.
Rahotanni sun nuna cewa kafin aiwatar da rabon tallafin, jami’an gidauniyar sun gudanar da bincike mai zurfi a kowane yanki domin tattara bayanan waɗanda suka fi cancantar amfana da shirin.
An bayyana cewa ɗaukar sunayen masu buƙatar tallafi ya gudana ne bisa la’akari da halin rayuwarsu da ƙarancin ƙarfinsu, domin tabbatar da cewa taimakon ya isa ga waɗanda aka fi buƙata. Haka kuma, an tsara rabon kayayyakin cikin tsari da natsuwa, lamarin da ya ba da damar gudanar da shirin cikin lumana da nasara.
Shugabannin gidauniyar sun jaddada cewa manufarsu ita ce rage raɗaɗin talauci da kuma inganta rayuwar al’umma ta hanyoyi daban-daban. Sun ƙara da cewa an daɗe ana gudanar da ayyukan jin kai a fannoni da suka haɗa da tallafin abinci, ilimi da sauran abubuwan more rayuwa, tare da mayar da hankali kan taimakawa masu ƙaramin ƙarfi a lokutan da suka fi buƙata.
Shugabar kwamitin amintattu na gidauniyar, Hajiya Lauratu Ado Diso, tare da shugaban gidauniyar na ƙasa, Dokta Abdullateef Abdulkadir, da sauran ma’aikata, an bayyana su a matsayin jajirtattu masu kishin al’umma, waɗanda ke tafiyar da ayyukan jinƙai bisa gaskiya da riƙon amana.
Masu nazarin harkokin jinƙai sun ce tsare-tsaren da gidauniyar ta shimfiɗa suna taimakawa wajen gano masu buƙata na haƙiƙa, tare da tabbatar da cewa tallafi ya isa ga sahihan waɗanda aka nufa. Sun kuma ce irin wannan tsari na gaskiya da tsabtace aiki ya kamata ya zama abin koyi ga sauran ƙungiyoyin agaji a faɗin ƙasar nan.
A ƙarshe, an yi kira ga al’umma da su ƙara fahimtar muhimmancin ayyukan jinƙai da irin gudunmawar da ƙungiyoyi irin Hazras ke bayarwa wajen saukaka rayuwar masu ƙaramin ƙarfi, tare da jaddada cewa gidauniyar za ta ci gaba da tsayawa kan manufofinta na taimakon al’umma ba tare da gajiyawa ba.
