Yadda rasuwar Alhaji Danlami Mai Goro ta girgiza al’ummar jihar Legas

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Rasuwar marigayi Alhaji Danlami Zubairu Mai Goro Zuwo ta girgiza al’ummar Hausawa mazauna Jihar Legas da ma jihar Kano baki ɗaya, bayan da Allah Ya karɓi rayuwarsa a ranar Lahadin da ta gabata a birnin Legas, bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Marigayin, ɗan asalin ƙaramar Hukumar Kiru a Jihar Kano, ya shafe shekaru da dama yana sana’ar kasuwanci a Legas, inda ya zama ɗaya daga cikin manyan jagororin ‘yan kasuwar kayan yarbawa a Kasuwar Mile 12 International Market. 

A rayuwarsa, ya taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kan ‘yan kasuwa masu shigo da kayan miya daga jihohin Arewa zuwa Legas domin sayarwa, musamman kayan kamar kubewa, yalo, alayyahu da sauran kayan amfanin yau da kullum.

Kafin rasuwarsa, marigayin shi ne jagoran ɓangaren kawo cigaban kasuwancin kayan yarbawa a kasuwar Mile 12, inda ya yi fice wajen taimakon ‘yan uwansa da karfafa hadin kai a tsakaninsu.

Ya rasu yana da shekaru 70 a duniya, ya bar mata biyu, ‘ya’ya bakwai – maza biyu da mata biyar – tare da jikoki da dama. ɗaya daga cikin ‘ya’yansa maza, Zubairu Danlami, na karatu a makarantar Polytechnic ta Kaduna.

An gudanar da jana’izarsa bisa koyarwar addinin Musulunci, inda aka yi masa addu’o’i da fatan Allah Ya jiƙansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, tare da sanya shi cikin Aljannatul Firdausi.

A yayin jana’izar, tawagar ‘yan kasuwar Mile 12 daga Legas, ƙarƙashin jagorancin shugaban kasuwar, Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam, sun yi tattaki zuwa mahaifarsa a Jihar Kano domin gabatar da ta’aziyyarsu ga iyalai da ‘yan uwa. Cikin tawagar har da babban magatakardan kasuwar, Alhaji Idris Balarabe, shugaban ƙungiyar dattawan kasuwar, Alhaji Isa Muhammed Mai Shinkafa, da tsohon shugaban kasuwar, Alhaji Haruna Muhammed Tamarke Mai Dankalin Turawa.

Bayan sun kammala ta’aziyya ga iyalai da makwabta, tawagar ta ziyarci mahaifin marigayin, Alhaji Zubairu Mai Goro, wanda ya haura shekaru ɗari a duniya. A wajen ziyarar, tsohon ya bayyana kyawawan halaye da ɗabi’un dansa, yana mai cewa ya kasance mutum mai addini, haƙuri da son taimakon al’umma.

Sakataren gudanar da harkokin kasuwancin ɓangaren kayan yarbawa a Kasuwar Mile 12, Alhaji Garba Garus, tare da sakataren kudi na ɓangaren, sun jaddada cewa marigayin mutum ne mai tausayi da daukar nauyin jama’a, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar al’umma da kasuwanci cikin gaskiya da riƙon amana.

Al’umma da dama sun bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga kasuwar Mile 12 da ma al’ummar Hausawan Legas gaba ɗaya, tare da addu’ar Allah Ya jiƙansa da rahama, Ya ba iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.

By ukarofi