Daga AISHA ASAS
*Gidauniyar Kannywood ta yi jimamin rasuwar sa
*An rufe ofishin Abnur da ke Kano har zuwa kammala addu’ar kwanaki 7
*Arewa Cultural Group ta yi alhinin rasuwar Nura Shariff
*ABNUR da masu ruwa da tsaki sun dakatar da ayyuka don girmama marigayin
Masana’antar fina-finai ta Kannywood ta shiga cikin babban alhini yayin da gidauniyar Kannywood da ƙungiyoyi daban-daban suka bayyana kaɗuwar su tare da alhini game da rasuwar tsohon jarumi kuma ƙwararren manajan shirye-shirye, Nura Shariff.
Marigayin ya shahara wajen aiki a kamfanin Abdul Amart na ABNUR Entertainment, inda ya taka rawar gani a shirya fina-finai da horar da taurari masu tasowa, tare da tabbatar da cewa kowanne aiki da yake jagoranta ya gudana cikin tsari da ƙwarewa.
Gidauniyar Kannywood ta bayyana cewa Shariff ƙwararren mai fasaha ne wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa a bayan fage, lamarin da ya taimaka wajen samar da fina-finai masu nasara a masana’antar. A matsayinsa na jarumi a kamfanin Iyantama a shekarun ’90s, ya nuna ƙwarewa, hazaƙa, da sadaukarwa, abin da ya sa ya samu ƙauna da girmamawa daga masu kallo da abokan aiki.
Daraktan Yaɗa Labarai na gidauniyar, Yakubu Liman, ya ce: “Shariff ya kasance jagora mai nagarta, mai kulawa da inganci, kuma kowane aiki da ya jagoranta ya samu nasara.”
ƙungiyar Mainagge Arewa Cultural Group Limited ta kuma bayyana Nura Shariff a matsayin jajirtacce, mai kawar da kai, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa ga ci-gaban masana’antar fina-finai ta Kannywood. Ta ce, kirki da hikimomin marigayin za su ci gaba da zama ababen tunawa da koyi ga taurari da abokan aiki.
A ɓangaren kamfanin ABNUR Entertainment da General Media Solutions, an ɗauki matakai na musamman domin girmama marigayin:
Ofishin ABNUR da ke Kano zai rufe har zuwa kammala addu’ar kwanaki 7.
Duk wani aiki na waje (shooting), tallace-tallace, da nunin fina-finai za a dakatar da su har zuwa bayan addu’ar kwanaki 40.
Duk wani shiri da aka tsara za a ɗage shi har sai bayan kwanaki 40.
Manajar kamfanin, Amina Adam, ta ce: “Mun ɗauki waɗannan matakai ne domin girmama Nura Shariff da ba wa ma’aikata da abokan hulɗa damar alhinin wannan babban rashi.”
Shariff zai riƙe matsayin abokin aiki na gari, jagora abin dogaro, kuma aboki ga mutane da dama a masana’antar. An yi addu’ar Allah Ya jikan sa da rahama, Ya gafarta masa, Ya kuma bai wa iyalai da abokan aiki haƙurin jure wannan babban rashi.
Marigayin ya bar gado mai yawa ga masana’antar Kannywood, daga ƙwarewarsa a aikin jarumi da shirya fina-finai, zuwa yadda ya taimaka wajen haskaka taurari masu tasowa. Hakan kuwa na tabbatar da cewa abinda ya bari zai ci gaba da kasancewa jagora da misali ga masu tasowa.
