Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, ya bayyana cewa ana gudanar da cikakken binciken ƙwararru kan Kamfanin Mai na ƙasa (NNPCL) domin tantance yadda ake cire kuɗaɗen shiga daga man fetur kafin su isa Asusun Tarayya.
Edun ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, inda ya yi wa masu ruwa da tsaki bayani kan sabbin matakan da gwamnati ke ɗauka wajen gyara tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce binciken yana gudana ne bisa umarnin taron Kwamitin Raba Kuɗaɗen Tarayya (FAAC), wanda ya nemi a zurfafa bincike kan duk wasu kuɗaɗen da ake cirewa daga man fetur.
A cewarsa, ana gudanar da binciken ne tare da aiwatar da sabon umarnin shugaban ƙasa, wanda ya tanadi cewa wasu takamaiman kuɗaɗen shiga daga ɓangaren mai da iskar gas su riƙa shiga kai tsaye cikin Asusun Tarayya, ba tare da tsayawa a wasu matakai ba.
Ministan ya bayyana cewa binciken na duba nau’o’in caji da ragi daban-daban da ke rage adadin kuɗaɗen da ya kamata su kai ga Gwamnatin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.
Ya ce a baya Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta umurci wani ƙaramin kwamiti da ya nazarci batun kuzin tattarawa da sauran caje-caje da ake yi daga Asusun Tarayya.
Edun ya ƙara da cewa, bisa sabon umarni, kuɗaɗe uku za su riƙa shiga kai tsaye cikin Asusun Tarayya: kuɗin gudanarwa (management fee), asusun bunƙasa yankunan gaba (frontier fund), da kuma tarar ƙone iskar gas (gas flare penalty).
Ya jaddada cewa wannan mataki ba zai hana ko daƙile duk wata doka ko bincike da ke gudana a Majalisar Dokoki ba, sai dai yana da nufin ƙara gaskiya, sahihanci da riƙon amana a tsarin kuɗaɗen shiga na ƙasa.
A cewarsa, an kafa wani kwamiti da ya ƙunshi wakilan gwamnatin tarayya da na jihohi domin tabbatar da aiwatar da wannan umarni yadda ya kamata, kuma ana sa ran zai fara zama a mako mai zuwa.
Ministan ya nuna kwarin gwiwa cewa haɗuwar wannan bincike na kwararru da sabon umarnin shugaban ƙasa zai warware dogon cece-kuce da ake yi kan zargin jinkirin miƙawa da kuma rashin cikakken bayani kan kuɗaɗen shiga daga ɓangaren mai.
Ya danganta matakin da babban shirin gyaran kuɗi na gwamnati, yana mai cewa a wannan lokaci da ribar lamuni ta duniya ke ƙaruwa kuma sararin bashin ƙasa ke taƙaita, ya zama wajibi Nijeriya ta mayar da hankali kan tattara kuɗaɗen cikin gida maimakon dogaro da bashin da ba ya samar da kuɗin da zai biya kansa.
Ya gargaɗi cewa yawan biyan bashin na rage damar kashe kuɗi a muhimman fannoni kamar kiwon lafiya, ilimi da gine-ginen more rayuwa.
