
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani matashi mai kimanin shekaru 21 ya rasu bayan zargin mahaifinsa da daɓa masa makami a yankin Umarari da ke Birnin Maiduguri a Jihar Borno.
A cewar rahotanni, al’amarin ya faru ne a ranar 25 ga Fabrairu da misalin ƙarfe 9 dare a lokacin da wani mai suna Ciyaman Mai Maya da ba a kai ga tantance shekarunsa ba, ya samu sa’in’sa da ɗansa, Alhaji Mohammed Lawan.
A yayin hatsaniyar, an zargi uban da saran ɗan nas har sau biyu a bayansa.
A lokacin da jami’an ‘yan sanda suke halarci wajen da abin ya faru, sun samu matashin kwance cikin jini, inda ɗauki shi hoto tare da gaggauta garzayawa da shi Asibitin State Specialist da ke birnin.
A safiyar 26 ga watan ne aka tabbatar da rasuwar matashin a lokacin da ake tsaka da ba shi kulawa.
Tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa a baza komar neman mahaifin ruwa-a-jallo domin kamo shi don ya fuskanci hukuncin da doka ta tanada.
Kazalika, ƙwararren masanin harkar tsaro, Zagazola ya bayyana cewa Cibiyar binciken manyan laifuka ta jihar SCID tana bincike akan al’amarin.
