Majalisar Dattawa na ƙoƙarin tabbatar da ‘yan sandan jihohi a hukumance kafin ƙarshen 2026

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Dattawa ta ce za ta kammala aiki akan gyaran kundin tsarin mulki na 1999 domin ba wa jihohi damar kafa rundunar ‘yan sanda kafin ƙarshen shekarar 2026.

Kakakin majalisar, Sanata Yemi Adaramodu ne ya shaida wa manema labarai hakan, inda ya ce za su koma kan aikin gyaran kundin tsarin mulkin nan da mako mai zuwa yayin da aka dawo zaman majalisar.

Wannan mataki na zuwa ne bayan buƙatar da Shugaba Bola Tinubu, ya miƙa wa Majalisar Dokoki ta ƙasa domin fara shirin gyaran kundin tsarin mulki don samar da ‘yan sandan jihohi.

Gwamnatin Tarayya na shirin ɗaukar matakin ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin magance matsalolin tsaro da ke addabar sassan Nijeriya.

By Babaji