
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni daga yankin Gabas ta Tsakiya sun bayyana cewa an sake jin ƙarar fashe-fashe masu ƙarfi a sararin samaniyar biranen Dubai (UAE) da Doha (Qatar) a yau Lahadi.
Wannan shi ne rana ta biyu a jere da yankin ke fuskantar hare-hare tun bayan kisan shugaban Iran, Ali Khamenei.
Mazauna biranen sun ce sun ji ƙararrakin da suka girgiza gine-gine, wanda ake kyautata zaton na kakkaɓo makaman linzamin Iran ne da tsarin kariya na kasashen ke yi.
An tabbatar da cewa harin daren jiya ya janyo gobara a tsibirin Palm Jumeirah da kuma ɓarna kaɗan a filin jirgin saman Dubai (DXB), inda mutane hudu suka jikkata.
A birnin Doha, wasu makaman sun fada kusa da unguwannin mazauna, inda mutane takwas suka samu raunuka.
Tuni dai manyan kamfanonin jiragen sama irin su Emirates da Qatar Airways suka dakatar da zirga-zirga har sai zuwa ƙarfe 3 na rana.
Gwamnatin UAE ta fitar da saƙon gaggawa ga mazauna ƙasar da su nemi mafaka kuma su nisanci wuraren da ake da fargabar hari akansu.
