Yaƙin Iran da Amurka/Isra’ila: Amurka ta umarci ‘ya’yanta a Isra’ila da ƙasashe 13 na Gabas ta Tsakiya su fice

Spread the love

Gwamnatin Amurka ta umarci jama’arta da ke zaune a yankin gabas ta tsakiya ciki har da jami’an ofisoshin jakadancin ƙasashen da su gaggauta barin yankin don komawa gida sakamakon tsanantar hare-haren Iran.

Haka na zuwa ne yayin da ofishin jakadancin Amurkan a Isra’ila ya ce ba zai iya ɗaukar nauyin fitar da Amurkawan daga Tel Aviv ba face su yi amfani da motocin safa wajen isa iyakar ƙasar da Masar.

Tuni Amurkan ta kulle ofisoshin jakadancinta da dama a yankin na gabas ta tsakiya ciki har da na birnin Riyadh wanda Iran ta kaiwa hari daga daren jiya zuwa wayewar garin yau da kuma ya haddasa ɓarna mai yawa.

Amurka ta nemi jamarta su yi amfani da jiragen ƴan kasuwa wajen barin yankin a wani yanayi da sararin samaniyar yankin baki ɗaya ke fuskantar barazanar hare-haren Iran.

A gefe guda Ofishin jakadancin Amurka da ke Isra’ila ya buƙaci jami’an ofishin da su samarwa kansu hanyar fita daga ƙasar kasancewar ba zai iya jagorantar fitar da su daga yankin ba.

Ma’aikatar ta buƙaci waɗanda ke son fita daga Isra’ilar da su yi amfani da motocin safa-safa wajen isa iyakar ƙasar da Masar don samun tsira.

By Babaji