
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kamfanin shirya finafinai na Abnur Entertainment ya miƙa godiya ta musamman ga ɗaukacin mambobin masana’antar Kannywood bisa alhininsu ga rasuwar ma’aikatacinsa, Nura Shariff.
A wata takarda da shugabancin kamfanin ya fitar, ya ce “Muna godiya ga waɗanda suka zo har gida domin ta’aziyya, waɗanda suka halarci taron addu’a, waɗanda suka kira ta waya, da kuma waɗanda suka wallafa saƙonnin ta’aziyya a kafafen sada zumunta.”
A cewarsa, hakan ya nuna cewa marigayi yana da daraja ta musamman, don haka ya yi godiya da fatan samun sayayya mai kyau ga dukkan waɗanda suka jajenta.
“Lallai kun nuna mana cewa marigayi ba karamin matsayi yake da shi a zukatan al’umma ba. Allah Ya saka muku da alheri, Ya maida muku da fiye da abin da kuka yi.”
Haka kuma, Kamfanin ya yi godiya ta musamman ga jaruma Hadiza Gabon na zuwa ta’aziyya da kuma bayar da kyautar N400,000 ga iyalan marigayin.
“Wannan abin alheri ba zai taba mantuwa ba. Allah Ya saka mata da aljanna, Ya kara mata ɗaukaka”, inji sanarwar.
Kazalika, ta yi godiya ga babban jarmu kuma Darakta Manaja na Huizenga Kula da Finafinai ta Ƙasa (NFC), Ali Nuhu, wanda bayan halartar taron addu’a ga mamacin, kuma ya bayar da kyautar N500,000 ga iyalansa.
“Wannan karamci da kulawa sun kara nuna zumunci da ƙaunar juna a tsakaninmu. Allah Ya saka masa da mafificin alheri.”
A ƙarshe, Abnur ya yi addu’ar “Allah Ya jikansa Nura Sharu, Ya gafarta masa, Ya sa Aljannatul Firdaus ta zama makomarsa, Ya kuma haɗa mu da shi a aljanna.”









