
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni sun bayyana cewa, Iran ta kai hari da jirage marasa matuƙa akan Ofishin Jakadancin Amurka da ke Riyadh, babban birnin Saudiyya.
An ga yadda harin ya haddasa ƙaramar gobara a gine-ginen ofishin, sai dai ba a samu asarar rai ba.
Tun dai ofishin jakadancin ya dakatar da ayyukan bada biza da sauran hidimomi a Birnin, Jeddah da Dhahran tare da gargaɗin ’yan ƙasa da su guji wurin domin tsaron rayukansu.
Harin na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin yankin ke ƙara tsananta tsakanin Iran da Amurka da Isra’ila.
A nata ɓangaren, Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta mayar da martani da kakkausar suka game da harin, inda a wata sanarwa ta ce tana yi alla-wadai da abin da ta kira da harin “cin amana”.
Ta kuma ce masarautar ta sake jaddada ‘yancinta na ɗaukar dukkan matakai don kare kanta da muradunta, game da zaɓin mayar da martani ga duk wani hari da aka kawo mata.
