Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Shugaban Jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya reshen ƙaramar hukumar Kura a Jihar Kano, Hon. Nasidi Danbalanti Kura, ya bayyana jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin jagora mai hangen nesa da tsayawa kan gaskiya da kuma son cigaban al’umma.
Danbalanti ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da sabbin shugabannin jam’iyyar NNPP a ƙaramar hukumar Kura, wanda aka gudanar a hedikwatar Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kura, Madobi da Garin Malam, Hon. Umar Yusuf Datti Kura, a ranar Asabar.
Ya ce al’ummar ƙaramar hukumar Kura na da cikakken goyon baya ga jagoran tafiyar Kwankwasiyya, inda ya tabbatar da cewa duk wanda Kwankwaso ya tsayar a zaɓe mai zuwa shi ne za su mara wa baya.
A cewarsa, jama’ar yankin na da ƙwarin gwiwa cewa jam’iyyar za ta sake komawa kan madafun iko a zaɓe mai zuwa.
Danbalanti ya kuma yi kira ga sabbin shugabannin jam’iyyar da aka rantsar da su da su yi aiki tukuru domin ƙarfafa jam’iyyar daga matakin unguwa har zuwa matakin ƙasa.
A nasa jawabin, tsohon mai bai wa gwamnan Kano shawara kan harkokin koyar da sana’o’i, Hon. Ado Hassan “Asha Falala”, ya taya sabbin shugabannin murna tare da jaddada muhimmancin riƙe amanar da al’umma suka dora musu.
Ya ce dole ne su yi aiki da gaskiya domin jam’iyyar ta samu nasara tare da ci gaba da gudanar da ayyukan raya ƙasa.
Shi ma Hon. Gambo Salisu Kura, shugaban matasan Kwankwasiyya a yankin, ya yi kira ga matasa da su shiga tafiyar Kwankwasiyya domin a cewarsa ita ce hanya mafi dacewa da za ta kai ƙasar nan ga cigaba.
Ya ce tafiyar Kwankwasiyya tafiya ce ta matasa, don haka ya bukaci su fito su mara wa jagoransu da sauran ‘yan takara baya domin samun nasara a zaɓe mai zuwa.
Da yake zantawa da manema labarai bayan rantsar da su, Ubale Musa, shugaban jam’iyyar a mazabar Danhassan, ya bayyana farin cikinsa bisa amincewar da al’ummar mazabar suka yi da shi domin jagorantar su.
Ya yi kira ga al’ummar yankin da su fito su yi rijistar katin zaɓe domin a cewarsa ta wannan hanya ce kawai za su iya kawo sauyi da cigaba a yankin.
Haka kuma ya yi kira ga hukumomin gwamnati na ƙaramar hukuma da na jiha da su taimaka wajen gyaran hanyar Danhassan zuwa Kunshama, Danga har zuwa Dukawa, wadda ya ce ta lalace matuƙa.
Ya bayyana cewa yankin na da yawan manoma, kuma lalacewar hanyar na janyo musu matsala wajen fitar da amfanin gonarsu musamman a lokacin damina.
Ya kuma ce wannan sabon tsarin shugabancin jam’iyyar ya biyo bayan sauya shekar wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC a kwanakin baya.
