ADC ta rabu biyu yayin da Kudu maso Kudu ta mara wa Amaechi baya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHHAMMAD

Taƙaddamar neman tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC gabanin zaɓen 2027 ta fara ɗaukar zafi bayan manyan masu ruwa da tsaki da shugabanni na jam’iyyar a yankin Kudu maso Kudu sun fito ƙarara sun bayyana goyon bayansu ga tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran fafatawa mai zafi a cikin jam’iyyar, lamarin da zai iya jefa ƙalubale ga sauran masu neman tikitin daga Kudu, ciki har da Peter Obi, wanda ake kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ‘yan takara.

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, John Odigie-Oyegun, ne ya bayyana wannan matsaya a taron tuntuɓa na shugabannin ADC na Kudu maso Kudu da aka gudanar a birnin Benin, Jihar Edo.

A cewarsa, Amaechi ya yi amfani da taron wajen sanar da shugabannin yankin a hukumance aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.

Odigie-Oyegun ya ce shugabannin yankin sun nuna jin daɗinsu da yadda Amaechi ya fara neman shawarar yankinsa kafin ya fara shimfiɗa tsarin yaƙin neman zaɓe a faɗin ƙasa. Ya bayyana cewa mahalarta taron sun cimma matsaya guda, inda suka ƙuduri aniyar bai wa Amaechi dukkan goyon bayan da yake buƙata domin cimma burinsa.

Rahotanni sun nuna cewa shugabannin yankin za su ci gaba da gudanar da irin waɗannan tarurruka domin daidaita matsayinsu da ƙarfafa tasirinsu a cikin jam’iyyar, musamman yayin da ake shirin fuskantar zaɓukan fidda gwani.

Tun a watan Yulin 2025 ne Amaechi ya bayyana aniyarsa ta yin takara, inda ya yi alƙawarin yin wa’adin shekaru hudu kacal idan ya samu tikitin ADC kuma ya lashe zaɓen 2027. Ya jaddada bukatar mutunta tsarin karɓa-karɓa na mulki, yana mai cewa ya kamata Kudu ta kammala wa’adin shekaru takwas kafin a mayar da mulki zuwa Arewa.

Amaechi ya taɓa neman tikitin shugaban ƙasa na APC a 2022, amma ya sha kaye a hannun Shugaban ƙasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu. Duk da cewa wasu ‘yan takara sun janye domin mara masa baya, Amaechi ya tsaya takararsa har zuwa ƙarshe, inda ya zo na biyu.

Yunƙurin sa na baya-bayan nan a ƙarƙashin ADC na nuni da sabon yunƙuri na komawa takarar shugabanci, wannan karon a wata sabuwar jam’iyya.

A gefe guda kuma, jadawalin zaɓukan fidda gwani ya janyo muhawara. Hukumƙr Zaɓe mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta umurci jam’iyyun siyasa da su gudanar da zaɓukan fidda gwani tsakanin 23 ga Afrilu zuwa 30 ga Mayu, 2026. Sai dai ADC ta yi watsi da wannan jadawali, tana zargin cewa yana bai wa jam’iyyar mai mulki fifiko.

Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana jadawalin a matsayin wani shinge mai wahalar tsallakewa ga jam’iyyun adawa, musamman dangane da tanadin sashe na 77(7) na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda ya ce na iya hana jam’iyyar da ba ta cika sharuɗɗan miƙa rajistar mambobinta cikin lokaci ba damar tsayar da ɗan takara.

Yayin da shekarar 2027 ke ƙara matsowa, alamu na nuna cewa ADC za ta fuskanci tsauraran tattaunawa, ƙulla ƙawance da sake tsari a cikin gida, yayin da ‘yan takara ke fafutukar samun tikitin jam’iyyar.

By ukarofi