Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani ɗalibin likitanci mai karatu a mataki na 200 a Jami’ar Ibadan (UI), mai suna Ifeoluwa Wisdom Akinmade, ya rasu bayan zargin cewa ya sha maganin ƙwari a daren Lahadi.
Rasuwar ɗalibin ta fito ne cikin wata sanarwa da Shugaban ƙungiyar ɗaliban Likitanci ta jami’ar (UIMSA), Folusho Olu-Adegbola, da Sakatarenta, Babatunde Dauda, suka sanyawa hannu a ranar Litinin.
A cikin sanarwar, sun bayyana cewa marigayin ya rasu ne duk da ƙoƙarin gaggawar jinya da likitoci suka yi domin ceton rayuwarsa.
Sanarwar ta ce: “Cikin alhini da zuciya mai nauyi muke sanar da rasuwar dan uwanmu kuma abokin karatunmu, Ifeoluwa Wisdom Akinmade, mamba a ajin mataki na 200. A wannan lokaci na baƙin ciki, muna roƙon Allah Ya bai wa iyalansa da abokansa haƙuri, ƙarfi da natsuwa.”
Rahotanni sun nuna cewa an fara kai shi wani asibiti a cikin jami’ar kafin daga bisani a mika shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan (UCH), inda ya rasu bayan shafe sa’o’i yana cikin halin suma.
Jami’ar ta bakin kakakinta, Joke Akinpelu, ta buƙaci a tuntubi Shugaban Sashen Harkokin ɗalibai, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a samu ƙarin bayani daga ɓangaren jami’ar ba.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na UCH, Funmi Adetuyibi, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa an kawo ɗalibin ne bisa zargin shan maganin ƙwari da ake kira “Sniper,” kuma an yi duk mai yiwuwa domin cetonsa, sai dai bai rayu ba.
Wasu saƙonni da suka bazu a kafafen sada zumunta sun yi iƙirarin cewa marigayin ya ɗauki matakin ne sakamakon samun ƙaramin maki a jarrabawar tes, wato CA, sai dai babu wata sanarwa ta hukuma da ta tabbatar da wannan zargi.
Lamarin ya sake tayar da hankula kan batun lafiyar kwakwalwa da matsin lamba da ɗalibai ke fuskanta a cibiyoyin ilimi. ƙungiyoyin masu fafutukar kare rayuka sun jaddada buƙatar wayar da kai da samar da hanyoyin neman taimako ga matasa masu fama da damuwa ko fargaba.
Masana ilimi da masu ruwa da tsaki na kira ga ɗalibai da su riƙa neman shawara da taimako idan suna fuskantar ƙalubale, tare da jaddada cewa kashe kai ba mafita ba ce ga matsala.
Idan kai ko wani da ka sani na fama da tunanin cutar da kai, yana da muhimmanci a tuntuɓi iyaye, malamai, shugabannin addini ko kwararrun masu ba da shawara domin samun taimako cikin gaggawa.
