Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata jami’a ta Hukumar Tsaro da Kare Lafiyar Al’umma ta Nijeriya, wato Sibil Difens (NSCDC), ta rasu bayan wata motar aiki ta hukumar ta murƙushe ta yayin atisayen horaswa da aka gudanar a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Lamarin ya faru ne a lokacin wani atisayen nuna ƙarfi da ake kira “show of force” na rundunar mata ta musamman ta hukumar, wacce aka fi sani da Female Strike Force ko Female Sƙuad.
Bidiyon da ya yaɗu na tsawon daƙiƙu 58 ya nuna yadda wata baƙar mota mai ɗauke da rubutun “Female Sƙuad” ta wuce kan jami’ar, yayin da wata motar aiki ke biye da ita a baya.
A cikin bidiyon, an ga yadda abokan aikinta da wasu da ke kusa da wurin suka garzaya domin ɗaga ta, kafin a kwashe ta cikin gaggawa zuwa motar ɗaukar marasa lafiya. Sai dai daga bisani aka tabbatar da cewa jami’ar ta rasa ranta sakamakon munanan raunukan da ta samu.
Mai magana da yawun NSCDC, Afolabi Babawale, ya tabbatar da aukuwar lamarin da rasuwar jami’ar, yana mai cewa za a fitar da cikakken bayani game da sunanta da kuma yadda haɗarin ya faru a cikin wata sanarwa ta hukuma da za a fitar nan gaba.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya janyo cece-kuce a tsakanin ‘yan Nijeriya, inda da dama suka buƙaci a gudanar da bincike cikin gaskiya da ƙwarewa domin gano musabbabin haɗarin. Haka kuma, sun nemi a bayyana sakamakon binciken domin tabbatar da ɗaukar matakan da za su hana faruwar irin wannan mummunan lamari a nan gaba.
Masu sharhi na ganin cewa wannan al’amari ya sake jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin kariya da kulawa yayin atisayen horaswa, musamman a rundunonin tsaro, domin kare rayukan jami’ai da ma al’umma baki ɗaya.
