Tun a Nuwamba Isra’ila ta ke kitsa halaka Khamenei, inji Ministan Tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Tsaron Isra’ila, Isreal Katz, ya bayyana cewa tun a watan Nuwamba ƙasar ta ɗauki matakin halaka Shugaban Iran Ali Khamenei, inda ta shirya aiwatarwa bayan wata shida.

Hare-haren Amurka da Isra’ila sun yi sanadiyyar mutuwar Khamenei ne a sa’o’in farko na yaƙin da ƙasashen ke yi da Iran, wanda aka fara a ranar Asabar ɗin makon da ya gabata.

A yanzu yaƙin ya shiga mako na biyu ana gwabzawa wanda ya yi silar mutuwar jagororin ƙasar da kuma haddasa yaƙin shiyya inda Iran take kai farmaki a sassan Isra’ila, yankin Gulf da kuma Iraƙi yayin ita kuma Isra’ila ke kai nata akan na hannun daman Iran, wato Hizbollah a Lebanon.

A cewar Ministan, an aike wa Washington shirin, sannan aka ƙara bayar da muhimmanci a kai a lokacin da zanga-zanga ta ɓarke a Iran a watan Junairu.

Akan haka ne Isra’ila ta shiga fargabar Iran ta kai mata hari da kuma akan kadarorin Amurka da ke yankin gabas ta tsakiya, inji Ministan.

Isra’ila ta ce manufarta ita ce ta kawo ƙarshen dukkan wata barazana ta shirin makami mai linzami na Iran da kuma kawo sauyin gwamnatin. Saidai jagororin Iran sun nuna babu wata alama ta sauya tsarin mulkin ƙasarsu.

By Babaji