
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar kula da Harkokin Man Futur ta Ƙasa NMDPRA, ta ce hauhawar farashin litar fetur a Nijeriya na faruwa ne sakamakon ƙalubalen sauye-sauye da ake samu a kasuwannin duniya ƙarƙashin rashin kyan gudanar da fannin a ƙasar.
Kakakin hukumar, George Ene-Ita ya bayyana haka ga ‘yan jarida a Abuja yau Lahadi, inda ya yi tsokaci a game da ƙarin farashin fetur na kwanan nan.
A cewarsa matsi da kasuwannin duniya ke fuskanta musamman bisa la’akari da yaƙin da ake gwabzawa a Gabas ta Tsakiya, wanda ya shafi farashin mai da kasuwannin makamashi na duniya.
Wannan rikici ya sa farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya haura kusan dala $90 kan kowace ganga, lamarin da ya sa farashin fetur a wasu sassan Nijeriya ya kere N1,000 kan kowace lita, abin da ke kara tayar da hankalin jama’a kan hauhawar farashi da tsadar rayuwa.
Masu kula da tattalin arziki na gwamnatin Nijeriya (EMT) na nazarin hanyoyin da za a rage tasirin wannan lamari ga kasar, yayin da gwamnati kuma ke shirye-shiryen kwaso ‘yan Nijeriya da ke Iran, musamman ɗalibai, sakamakon ƙaruwar tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.
Masana sun yi gargadin cewa duk da cewa karin farashin mai a duniya na iya kara kuɗaɗen shiga na fitar da mai ga Nijeriya, hakan kuma na iya haifar da ƙarin farashin fetur a cikin gida, hauhawar farashi, da kuma tangarda ga harkokin kasuwanci.
