Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Wannan mako ga amsa ga wani matashi kan salon mulkin Sardauna da matashin ke da ra’ayin ba a yi adalci ba.
Shin Sardauna ya fifita wata kabila kan wata?
Ina ganin kai na taɓa yi wa tambaya don sanin kai Bature ne ko Bahaushe don na ga ka maƙala hoton wani mai jan kunne mai ƙananan idanu sanye da hana sallah. Da farko zan ce wallahi ban lura da rubutun ka ba sai yanzu kuma gaskiya ka yi dogon rubutu ko da kuwa kwafi ka yi. Na karanta rubutun kakaf ga amsa ɗaya bayan ɗaya.
1. Ka kawo batun “northernization policy” da ka kawo hujja daga litattafan wasu mutane irin wanda ka ce Treɓor Clark da ka iya rubuta ra’ayin sa kuma sai ma a 1987 bayan kusan muhimman wadanda a ka yi abun a idon su ma sun mutu. Ba ni da tabbacin adalcin mutumin nan. Ka kawo batun tsarin ya fifita Fulani nan ma ‘yan gidan sarauta, to ina sauran miliyoyi da ba ‘yan gidan sarautar ba? Su ma duk ‘yan tsiraru na gidan sarauta sun sha da rabon su kenan? Wallahi dasisa ce kawai ta makirci don tsarin na Sardauna shi ya taimaki duk ‘yan bokon Arewa daga kowace ƙabila kuma Musulmi da Kirista. Ka kawo wai Hausawa da ba su da alaƙa da Daular Sokoto ba su amfana ba da hakan ke nuna ashe akwai waɗanda su ka amfana hatta a wannan annamimancin. Matsalar ku ita ce waye Bahaushe kuma waye Bafulatani. Rarrabe mutanen nan na da alaƙa da son zuciyar bambancin addini. In ba shakiyanci ba wa zai kalli Sardauna ya ture shi daga Hausawa. Duk mutanen duniya na ganin Sardauna a matsayin uban Hausawa da sauran ƙananan ƙabilun Arewa.
2. Ka ce jihadin Shehu ya kawar da Sarakunan Hausawa da kawo Fulani inda abun ya ci gaba har zamanin Sardauna. Farko sam jihadin Shehu ba na Fulani ba ne amma don shi Bafulatani ne a ke yin sharri cewa na Fulani ne amma haƙiƙanin magana jihadin Musulunci ne. Baya ga Sarkin Gobir Yunfa da ya yaki Shehu har ya nemi kashe shi kowa ma ya huta, Shehu bai daga takobi ya yaƙi kowa ba. Kai abun da ya faru ma shi ne mutane kan yi tattaki su samu Shehu don neman jaddada Musulunci a yankunan su inda almajiran Shehu kan tafi don wannan aiki don sarakuna a Daular Shehu su ne limamai ba irin na yanzu na sarautar gargajiya ba. Shi ya sa kamar a Bauchi a ka samu Malam Yakubu wanda ba Bafulatani ba ne ya karɓi tuta ya taho nan kuma har yau zuriyar sa ke sarauta.
Ka kawo me ya sa Sardauna bai canja tsarin Sarauta ya mikawa jikokin waɗanda su ke kai gabanin Daular Shehu ba? Wannan ai rashin sanin tsarin mulkin siyasa ne da ke da bambanci da na soja. Sardauna fa ya zauna da gwamnan mulklin mallaka Sir Bryan Sharwood Smith mai wandon karfe har zuwa karɓar ‘yanci kuma tarihin gwagwarmayar tabbatar da adalci da ya yi na nan har da rashin yarda a ba da ‘yanci a 1958 don jiran sai ‘yan bokon arewa sun samu sosai ko sun shirya don kar wasu su mamaye mu su guraben aiki. Ba zai yiwu Sardauna na aiki da wakilan kowane sashe na Arewa ya wayi gari ya ce ya sauke sarakuna ya dawo da na asali kafin Daula ba. Shin ka ma san abun da ya biyo bayan kwabe Khalifa Sunusi da Sardauna ya yi daga sarautar Kano? In ba ka sani ba nemi tarihi. Kacokan fa daga ‘yancin kai a 1960 Sardauna shekara 4 da wata 4 da kwana 15 ya yi a matsayin Firimiya a ka yi ma sa kisan gilla tare da matar sa. Wasu fa mahaukata sun ɗauka Sardauna shekara 2000 ya yi ya na jagorantar Arewa.
3. Ka kawo Sir Abubakar Tafawa Balewa wai ya nuna kuskuren haɗe kudu da arewa a 1914 kuma ba ka kawo ƙarin bayani ba inda ka ce duk da haka Sardauna ya dage da cewa Arewa ɗaya ce. Yauwa hakan zai nuna ma ka gaskiyar magana yadda Sardauna ya rike ‘yan Arewa kakaf a matsayin mutum ɗaya ba bambanci. Wallahi maƙiya ne kawai su ke canja tarihin don jin haushin alaƙar Sardauna da Shehu da kuma jajircewa wajen ganar da marar sa addini a lokacin da su hɗda da maguzawan kan dutse su sauko su saka kaya da daina laftawa jikin su ganye ala ba shi su Musulunta ko su shiga addinin da su ke so. Nemi bayanan marigayi Danmasanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule kan Sarkin Kagoro. Kazalika ka soki abun da ka zaiyana da kanbama Arewa kan Hausawa. Idan mutum ya na mulki ba zai yiwu ya zama ya na da gefe ba kowa nasa ne. Shi ya sa fa kananan ƙabilun Arewa ke jin haushin Hausawa da cewa su na kiran su da ARNA. Hakan ya sa yau cikin nau’in Hausawan nan masu iƙirarin kare Hausa Zalla akwai waɗannan ƙabilun da ke son rusa Hausawa kakaf da dabarar wai su ne ma Hausawan. Wallahi gadar zare ce. Dattawan Arewa da ka ke magana kamar ƙungiyar NORTHERN ELDERS da Farfesa Ango Abdullahi ke jagoranta ba gwamnati ba ce amma majalisar waɗanda su ke kishin Arewa ne kamar yadda Yarbawa ke da Odua/Afenifere, Igbo ke da Ohaneze Ndigbo. Ga NORTHERN UNION ta marigayi Olu Sola Saraki. Ga ƙungiyar tuntuɓar juna ta Arewa ACF ƙarƙashin Chief Mamman Mike Ousman, ga gamayyar ƙungiyoyin Arewa ƙarƙashin Jamilu Aliyu Charanci da madugu Nastura Ashir Sharif. Kowa na ba da gudunmawa daidai gwargwado. Ba wanda sau curin masaki bai yi maganar mafita kan ƙalubalen ‘yan bindiga ba.
4. Ka ce Dokta Bala Usman a 1987 ya ce siyasar Arewa ta NPC da Sardauna ke ciki ta fifita masu alaƙa da sarauta ne. Daga nan ba ka ci gaba da sharhin na Dokta masanin tarihi ba sai ka ɗora da na ka cewa “wannan ya bar Hausawa talakawa a gefe ya kuma gina tsarin siyasa na ‘yan tsiraru masu iko” a nan in ya bar Hausawa talakawa a gefe ina tsarin ya kai masu kuɗi na Hausawa? Kazalika ina ya kai talakawa Fulani da sauran ƙabilu fiye da 200 na Arewa? Mu riƙa yin adalci da kaucewa bambance-bambancen da ba riba a wannan karni na mu na 21. Bambanci a zahiri da ke damun Arewa ba na Hausawa ko Fulani ko Kanuri ko wata ƙabila ba ne a wannan sashen bayani amma matsalar na daga takalmin ƙarfen ‘yan jari hujja kan talakawa na kowace ƙabila. Ko ka san tsamar masu kuɗi da talakawa ta sa talakawa jajircewa wajen zabar marigayi shugaba Buhari inda bayan ya hau a 2015 su ka dawo daga rakiyar sa don ba su tantance barcin makaho ba da farkawar sa ba?
Ka rufe da nuna Sardauna bai yi wa Hausawa wakilci ba kuma ba uban su ba ne. Hakan ya saba da yadda ka ce mulklin NPC ya fifita masu alaƙa da sarauta ne kuma ka san Arewa ba iya nan ƙasar Hausa mu ke da ita ba akwai masarautar Ilorin, Etsu Nupe a Neja, Aku Uka a Wukari, Sarkin Igala, Gbon Gwom Jos, Shehun Borno, Hama Bachama a Adamawa da sauran su. Ka ce dan siyasa har shakka ya ke yi ya ce shi ba Bafulatani ba ne, wannan ƙirƙirarriyar magana ce da sam ba ta da tushe bare makama. Gara ma ka kawo min masu amfani da addini a siyasa da batun ƙabilanci. Mu bar ɗan siyasa da dabarar sa ta neman ƙuri’a amma bisa tsarin mulki kowa ya na da haƙƙi daidai wa daida. A baya ba ‘yan siyasa kan ce in an zaɓe su za su kawo fonfon fura da nono ba. Ka ga ai ko ba su kawo ba yau ga kantunan fonfunan fura da nona barjak a Arewa, ko na kawo misali? Mutan Zuru fa duk a dalilin Sardauna su ka zama manyan jami’an sojan Nijeriya. Tambayi labarin ‘yan Lantang Mafia a Filato.
Yau ba sai ka aibanta wani ba za ka iya zama komai a Nijeriya daga kowace ƙabila ko addini ka fito. Ka duba misalin yadda Malam Ibrahim Shekarau ya zama gwamnan Kano bayan an ce ba shi da kowa sai Allah. Hatta Wazirin Adamawa Atiku Abubakar ɗan talakawa ne futuk amma ka ga yadda Allah ya daukaka shi. Mu Arewa duk ɗaya ne nuna bambancin ƙabilanci ba zai taimake mu ba. Ba wata riba da zan ci ko za ka ci in mu na tunani da sanya son zuciya ko ƙulla ƙiyayya da ƙirƙirar labarun karya.
KAMMALAWA
Shehu Mujaddadi ya koma ga Allah shekaru 208 da su ka shuɗe, Sir Ahmadu Bello ya koma ga Allah shekaru 59 da su ka shude. Idan ka duba ratar lokacin da a ka haife ka da lokacin da su ka mutu ma ba a magana sai ta kakanni. Me zai sa ba za mu daina sukar juna mu zauna lafiya ba. Fakewa da ‘yan bindiga ko ‘yan ta’adda da nuna su ke wakiltar wata ƙabila rankatakaf wata mummunar dasisa ce da makiya ke azzamawa don kawo fitinar da za ta hana ka iya wannan dogon rubutun a waya!. In ka zarge ni da ina marawa ‘yan ta’adda baya don ban shiga ƙungiyar ‘yan kwangila ba sai in ce ma ka ba irin labarin da ban yada na yaƙi da ta’addanci ba har labari na ɗauko kai tsaye a lokacin da ‘yan ta’adda su ka tare mu a hanyar Kaduna zuwa Abuja Allah ya sa da sauran shan ruwanmu. Kai menene ma riba ta in an caccake ni da sharri na marawa ‘yan ta’adda baya ni da ke zaune a birni ba ni da saniya ko ɗaya, saniya ta wannan alƙalami da na ke rubutu da shi kuma na tsaya ina rubutun don ba da gudunmawa ta ga Arewa da ta ba ni karatun firamare da sakandare kyauta.
