
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Sufurin Jiragen sama da Ci-gaban Sararin samaniya, Festus Keyamo, ya umarci a riƙa amfani da tsarin biya mai baki biyu a dukkan ƙofofin shiga filayen jiragen sama na Nijeriya, wanda zai fara aiki daga ranar Juma’a, 13 ga watan Maris, 2026.
Hakan na nufin za a riƙa karɓar kuɗi a yanayi na tsaba da kuma amfani da katin cirar kuɗi na banki, wato ATM.
Wannan na zuwa ne bayan umarnin dakatar da biya ta na’ura a makon da ya gabata daga Shugaba Bola Tinubu saboda cinkoso da hakan ke haifarwa.
Keyamo ya gana da jami’an Hukumar Kula da Filayen Jiragen saman Nijeriya (FAAN) da manyan jami’an ma’aikatar, inda suka cimma matsaya akan hanyoyin da za a bi wajen magance matsalolin cinkoson.
A yayin haka ne suka samar da cikakken tsarin biya ta na’ura a kowac ƙofa na filayen, lamarin da ka iya kawo ƙarshen biya ta tsaba.
Haka kuma, masu ababen hawa da ke ƙarƙashin tsarin katin FAAN Go Cashless za su cigaba da amfani da su har zuwa lokacin da za a fitar da sauyi a kai, kamar yadda sauran tsare-tsaren irin su POS da makamansu za,su kasance a shirye domin amfanin jama’ar.
Ya kuam kirayi al’umma da masu ababen hawa da su mallaki FAAN Go Cashless yayin da hukumar ke cigaba da ƙoƙarin inganta tsarin.
