Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rikicin da ya dabaibaye Iran da Israel bai samo asali daga yau ba. Ya samo tushe ne tun daga sauyin gwamnati da ya girgiza yankin Gabas ta Tsakiya a shekarar 1979, lokacin da juyin-juya halin Musulunci ya kawo ƙarshen mulkin Shah tare da kafa Jamhuriyar Musulunci a Tehran.
Amma kafin wannan lokaci, dangantakar ƙasashen biyu ta kasance mai kyau, har ma ana kallon Iran a matsayin ɗaya daga cikin ƙawayen ɓoye na Isra’ila a yankin.
Kawance a zamanin Shah:
A ƙarƙashin mulkin gidan sarautar Pahlavi, musamman a zamanin Shah Mohammad Reza Pahlavi, Iran ta kasance kusa da Amurka da ƙasashen yamma. A wancan lokaci, Isra’ila na neman abokan hulɗa a yankin da yawancin ƙasashen Larabawa suka ƙi amincewa da ita bayan kafuwarta a 1948. Iran, duk da adawarta ga rabuwar Falasɗinu, ta kasance ƙasa ta biyu mai rinjayen Musulmi da ta amince da Isra’ila bayan Masar.
Dangantakar ta ƙunshi hadin gwiwar tsaro, leƙen asiri da kasuwanci. Wannan ƙawance ya taimaka wa Isra’ila rage ƙawayen da ke adawa da ita, yayin da Iran ke amfana da goyon bayan Amurka a ɓangaren tsaro da tattalin arziki.
Juyin-juya halin Musulunci da sauyin alƙibla:
Komai ya sauya ne a 1979, lokacin da Ruhollah Khomeini ya jagoranci juyin-juya halin Musulunci, wanda ya hamɓarar da Shah tare da kafa sabuwar gwamnatin da ta ɗoru kan aƙidar adawa da Amurka da Isra’ila, saboda irin zaluncin da suke tafkawa a doran ƙasa. Sabuwar gwamnatin ta katse duk wata hulɗa da Isra’ila, ta kwace ofishin jakadancinta a Tehran, tare da miƙa shi ga wakilan Falasɗinawa.
Tun daga wannan lokaci, Iran ta ɗauki batun Falasɗinu a matsayin ginshiƙi na manufofinta na waje. Ta fara tallafa wa ƙungiyoyin da ke adawa da Isra’ila, ciki har da Hizbullah a Lebanon da kuma wasu ƙungiyoyi a Falasɗinu. Wannan mataki ya jefa ta cikin doguwar taƙaddama da Isra’ila, wadda ta fara kallon Iran a matsayin babbar barazana ga wanzuwarta.
Goyon bayan Amurka ga Isra’ila:
A duk tsawon wannan rikici, Amurka ta kasance babbar ƙawar Isra’ila. Tun daga kafuwar Isra’ila, Amurka ke ba ta goyon bayan siyasa, kuɗi da makamai. Wannan goyon baya ya ƙara ƙarfafa Isra’ila a fagen tsaro da diflomasiyya, musamman a Majalisar ɗinkin Duniya, inda Amurka ke amfani da iko domin kare muradunta.
Iran na kallon wannan goyon baya a matsayin wani ɓangare na abin da take kira da “zaluncin tsarin duniya” a kan al’ummar Falasɗinu. Hakan ya sa Tehran ke zargin cewa duk wani hari da Isra’ila ke kai wa yana samun kariya ko amincewar Amurka kai tsaye ko a fakaice.
Yaƙin sunkuru da hare-Hare na ɓoye:
A shekarun 1990 zuwa 2010, rikicin ya ɗauki sabon salo na “yaƙin sunkuru,” wato hare-haren da ba a bayyana hannu kai tsaye ba. A 1992, an kai hari kan ofishin jakadancin Isra’ila a Buenos Aires, abin da Isra’ila ta danganta da ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Iran. A ɓangare guda, Iran ta zargi Isra’ila da kashe masana nukiliyarta da kai hare-haren ta intanet kan cibiyoyinta.
Babban abin da ya fi tada jijiyoyin wuya shi ne shirin nukiliyar Iran. Isra’ila ta sha bayyana cewa ba za ta taɓa amincewa da Iran ta mallaki makamin nukiliya ba. Duk da cewa Iran ta dage cewa shirinta na zaman lafiya ne, Isra’ila da ƙawayenta na yamma sun yi zargin akasin haka.
Hare-Haren Syria da Lebanon:
Tun daga 2011, bayan ɓarkewar rikicin Syria, Isra’ila ta riƙa kai hare-hare kan wuraren da ta yi zargin Iran na amfani da su wajen jigilar makamai zuwa Hizbullah a Lebanon. Iran ta ɗauki wazannan hare-hare a matsayin cin zarafi da kuma keta huruminta.
Haka kuma, an samu hare-hare kan jiragen ruwa a Bahar Maliya da Bahar Rum, inda kowanne ɓangare ke zargin ɗayan da kai farmaki.
A farkon shekarar 2025, Isra’ila ta kai jerin hare-hare kan cibiyoyin da ta ce na nukiliyar Iran ne. Rahotanni sun nuna cewa wasu manyan jami’an dakarun kare juyin juya hali sun rasa rayukansu. Iran ta ɗora alhakin hare-haren kan Isra’ila tare da zargin Amurka da mara mata baya.
Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ali Khamenei, ya sha alwashin cewa Isra’ila za ta fuskanci martani mai tsauri. A martaninta, Iran ta harba makamai masu linzami zuwa wasu biranen Isra’ila, ciki har da Tel Aviv da Haifa, lamarin da ya janyo asarar rayuka da ɓarna.
Bayan dukka wannan, a daren Juma’ar da ta gabata, hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila sun yi ajalin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na ƙasar Iran, Sayed Ali Khamenei, wanda hakan ya fusata Iran da ma al’ummar duniya masu goyon bayan adalci da gaskiya.
Dama Iran ta shirya wa zuwan wannan lokaci, inda rahotanni suka ce an riga an tsara wanda zai gaji Khamenei da kuma da dama daga cikin manyan jagororn ƙasar.
Saboda haka har yanzu babu tabbas kan tasirin da kisan Khamenei da jagororin tsaron ƙasar zai yi ga wannan rikici.
Daga ɓangaren Iran, rikicin ba wai kawai batun siyasa ba ne, illa kuma kare waɗanda ake zalunta. Tehran na ganin kanta a matsayin mai kare Falasɗinu da kuma mai ƙalubalantar tasirin Amurka a yankin.
Masu goyon bayan Iran na cewa tsayin daka da ta yi ya hana Isra’ila da ƙawayenta mamaye yankin ba tare da ƙalubale ba. Suna kuma jaddada cewa dukkan hare-haren da Iran ke kaiwa martani ne kan hare-haren da aka fara kai mata.
Rikicin Iran da Isra’ila ya samo asali ne daga sauyin siyasa na 1979, amma ya zurfafa ne sakamakon siyasar yankin da kuma goyon bayan da Amurka ke bai wa Isra’ila.
Duk da haka, ainihin mafita ba za ta samu ba sai an magance tushen matsalar – batun Falasɗinu da kuma tsarin tsaro da ya dogara da ɓangaranci. Har sai an samu adalci da daidaito a yankin, rikicin zai ci gaba da kasancewa wata wuta mai ci a ƙasa, wadda ke iya tashi a kowane lokaci.
