Gudunmawar iyaye wajen nasarar ’ya’yansu a makaranta

Spread the love

Tare da BILKISU YUSUF ALI

Iyaye suna da rawar gani sosai wajen tabbatar da nasarar ‘ya’yansu a makaranta. Rashin kulawa ko rashin goyon baya daga iyaye kan iya shafar karatun ɗalibai ta hanyoyi da dama, yayin da kulawa da haɗin kai tsakanin iyaye da makaranta ke ƙara wa ɗalibai ƙarfi da ƙwarin gwiwa wajen cimma burinsu. 

Muhimman abubuwan da iyaye za su yi don taimakawa nasarar ‘ya’ya

1.Kulawa da yanayin karatu a gida

Iyaye su tabbatar cewa suna samar wa ‘ya’yansu wuri mai kyau da kwanciyar hankali domin karatu. Hakan yana taimakawa wajen mayar da hankali da samun sakamako mai kyau.

2. Taimakawa da kula da aikin gida (Homework)

Iyaye su kasance masu lura da aikin gida na ‘ya’yansu, su duba ko an yi aikin, su kuma taimaka idan akwai buƙatar hakan.

3.Hada kai da malamai

Yin hulɗa kai tsaye da malamai na makaranta don samun bayanai game da halin da ɗalibi ke ciki, da yadda za a magance matsalolin da suka taso.

4. ƙarfafa ‘ya’ya gwiwa

Iyaye su kasance masu ƙarfafa wa ‘ya’yansu gwiwa ta hanyar yabawa a duk lokacin da suka samu nasara ko suka yi ƙoƙari, hakan yana ƙara musu ƙwarin guiwa.

5. Horon rayuwa da ladabi

Baya ga karatu, iyaye su koya wa ‘ya’yansu ɗabi’u masu kyau kamar tsari, kiyaye lokaci, da ladabi wanda zai taimaka musu wajen yin kyakkyawan aiki a makaranta da kuma rayuwa gaba ɗaya.

6.Addu’a

Addu’a tana taka muhimmiyar rawa ko ma a ce ita ce ginshiƙi da iyaye ya kamata su wajabtawa kansu kan lallai su dage yi wa yaransu kan shiriya da samun ilimi mai albarka. 

7. Abokai da ƙawaye

Yana da matuƙar amfani kan sa idon iyaye su fahimci su waye abokan yaransu da kawayen ‘ya’yansu a aji da unguwa da na ma zumunci. Saboda son karatu da mayar da hankali a duk al’amuran rayuwa na yau da kullum. 

8. Tattali

Yana daga cikin abin da iyaye ya kamata su nusar da yaransu har da koya musu tattali da alkinta littafi da nuna muhimmancin littafi. Yin aka zai kimsa wa yara gane muhimmancin karatu musamman ma in har su ma iyayen masu sha’awar karatu ne to yaran su ma za su zama masu sha’awa. 

Tasirin gudunmawar iyaye

ɗalibai masu iyaye masu kulawa suna samun sakamako mafi kyau a makaranta.

Rage rashin halartar makaranta da jinkiri wajen kawo ayyuka.

Samar da yanayi mai kyau da kwanciyar hankali ga ɗalibi wanda ke ƙara masa ƙwarewa da natsuwa wajen karatu.

Iyaye na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar ‘ya’yansu a makaranta. Ta hanyar nuna kulawa, ƙarfafawa, da haɗin kai da malamai, iyaye na iya taimakawa wajen gina ƙarni mai ilimi da nagarta. Haka nan, wannan haɗin kai yana haifar da al’umma mai ci gaba da kwararru.

By ukarofi