Yadda waken soya ke rage tasirin tsufar fata

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Masu karatu ya ibada. Barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja. Sannunku da jimirin bibiyarmu. Allah Ya karbi idabunmu.

Idan Blueprint Manhaja ta makon da ya gabata ba ta wuce ku ba, za ku iya tuna mun faro bayyani kan irin tasirin da waken soya yake da fata da yadda yake taimakonta a yayin da ta shiga matsala ko take buƙatar taimako sakamakon gajiyawa ta shekaru. 

Kuma mun sanar da ku irin sinadarai da yake cikin sa da yadda suke warkar da wasu matsaloli.

A wannan makon za mu yi duba ne kan yadda yake tasiri wurin rage lalacewar da fata ke yi ta sanadiyar tsufa.

Kamar yadda muka faɗa, sinadaran Isoflavones da ake samu da yawa a cikin waken soya ayyukan da suke yi suna kamaiceceniya da irin aikin sinadaran halitta da ke aikin kula da lafiyar fata.

Fata ita ce sashen da yafi bayyana a jikin ɗan adam, kuma tana fuskantar sauye-sauye sakamakon shekaru, yanayi, gado da salon rayuwa. Yayin da shekaru ke ƙaruwa, fata na iya fara  bushewa, fara nuna layukan tsufa, rage kauri irin yadda aka saba ganin fata, raunin katangar kariya musamman ga mata bayan daina jinin al’ada, raguwar sinadarin mata na janyo raguwa a samar da kolajin, wanda shi ne ginshiƙin ƙarfi da taushin fata.

Bincike ya nuna cewa, isoflavones na waken soya na taimaka wa rage wannan tasiri, ko ga mata kafin ko bayan daina jinin al’ada.

By ukarofi