‘Yan Majalisar Wakilai uku sun koma APC daga PDP

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

‘Yan Majalisar Wakilai guda uku sun fice daga Jam’iyyar adawa ta PDP tare da koma wa cikin mai mulki (APC).

‘Yan majalisar sune Inuwa Garuba (Yamaltu/Deba ta Gombe), Abdullahi El-Rasheed (Dakku/Nafada ta Gombe), da kuma Mohammed Audu (Karim Lamido Lau/Ardo-Kola ta Taraba).

Kakakin majalisar, Tajudeen Abbas ya sanar da haka a yau Laraba yayin zaman majalisar.

A saƙonnin ‘yan majalisar, sun bayyana dalilin ɗaukar matakin nasu a matsayin rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa acikin tsohuwar jam’iyyar tasu da rarrabuwar kai a tsakanin ‘ya’yanta.

Sauyin jam’iyyar na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da samun sauye-sauyen siyasa a majalisar dokokin Nijeriya, inda wasu ’yan majalisa ke komawa APC daga jam’iyyun adawa.

By Babaji