Ɗan Majalisar Zamfara ya raba buhunan abinci 7,000 ga al’ummarsa

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ɗan Majalisar Wakilai, mai wakiltar ƙananan hukumomin Bakura da Maradun a jihar Zamfara, Hon. Mohammad Sani Ahmad (Abba Yariman Bakura) ya raba buhunan abinci iri-iri guda 7,000 ga alummar mazaɓarsa a matsayin tallafin watan Ramadan.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da kayayyakin abincin a garin Bakura ƙaramar hukumar Bakura a yau Laraba, Hon. Abba ya bayyana cewa waɗanda suka amfana da tallafin sun haɗa da, ƙungiyoyi masu rauni, ‘yan gudun hijira, marayu, masu buƙata ta musamman da magoya bayan sa.

A cewarsa, kayayyakin sun haɗa da, buhunan shinkafa 3,000, buhunan gero 2,000, buhunan sukari 1,000, da kwalaye 600 na madara.

Hon. Abba ya ƙara da cewa manufar karamcin shine domin tabbatar da cewa alummar mazaɓarsa sun gudanar da azumi cikin sauƙi.

Da yake jawabi, shugaban kwamitin rabon kayan, Alhaji Aliyu S. Pawa, ya yaba wa Hon. Abba Yariman Bakura kan damuwarsa ga walwalar alummar mazaɓarsa.

Hakazalika wasu masu ruwa da tsaki a yankin, Alhaji Yakubu Gado Maradun da Mohammed Sani Dantsito Rini, sun yaba da ƙoƙarin ɗan majalisar, inda suka bayyana karamcin a matsayin wanda ya dace.

By ukarofi