Daga SANI AHMAD GIWA, Abuja
Jami’an Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC), sun yi wa Babban Alƙalin Kotun Tarayya, Justice John Tsoho, tambayoyi na tsawon sa’o’i a ranar Talata kan wasu kuɗaɗen dalar Amurka 160,000 da aka gano a hannun matarsa.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an EFCC sun gayyaci alkalin ne domin yi masa tambayoyi dangane da kuɗin da aka ce an samu a hannun matarsa yayin wata tafiya da take yi.
Wani rahoto da SaharaReporters ta wallafa ya ambato wata majiya daga EFCC na cewa an yi wa alƙalin tambayoyi na tsawon lokaci domin ƙarin bayani kan lamarin.
Rahoton ya biyo bayan wani bincike da SaharaReporters ta wallafa a ranar Lahadi cewa jami’an EFCC sun tare matar alƙalin yayin da take kan hanyarta ta zuwa Jihar Benue.
Majiyoyi sun ce bayan an tare ta, an mayar da ita Abuja, inda aka ce jami’an EFCC sun gano cewa tana ɗauke da kuɗi har dala 160,000 a lokacin da aka tsayar da ita.
Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken bayani a hukumance ba dangane da asalin kuɗin da kuma dalilin tafiyar da ta yi.
Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara sa ido kan alƙalin, bayan wasu zarge-zarge da suka shafi bayyana kadarori.
A wani ɓangare kuma, ana sa ran Justice John Tsoho zai gurfana a gaban Hukumar Code of Conduct Bureau (CCB) a ranar 16 ga Maris, 2026, kan zargin ƙin bayyana wasu kadarorinsa kamar yadda doka ta tanada.
Wata takardar ƙorafi ta zargi alƙalin da karya dokar Code of Conduct ta hanyar kin bayyana wasu asusun banki guda uku da ake zargin yana da su a United Bank for Africa (UBA) da kuma wani asusu a Access Bank.
Idan har hukumar CCB ta tabbatar da akwai hujjojin farko kan zargin, za ta iya gurfanar da alkalin a gaban kotun Code of Conduct Tribunal domin ci gaba da shari’ar.
Dokar Nijeriya ta tanadi cewa idan aka samu wani jami’in gwamnati da laifin boye kadarori ko bayyana su ba cikakke ba, yana iya fuskantar hukuncin da ya haɗa da ɗaurin shekaru har 10 a gidan yari da kuma hana shi rike mukamin gwamnati na tsawon shekaru 10.
A cikin wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai ta Kotun Tarayya, Catherine Christopher, ta fitar a ranar Litinin, ta ce Babban Alkalin kotun ya nuna shirinsa na yin cikakken haɗin kai da hukumar CCB kan gayyatar da ta yi masa.
Sanarwar ta ƙara da cewa alƙalin zai gurfana a gaban hukumar tare da lauyansa Kanu Agabi (SAN), wanda a halin yanzu yake wajen kasar nan domin jinya.
Kotun ta bayyana cewa babban lauyan ya nuna shirinsa na rakiyar alkalin zuwa gaban hukumar da zarar ya dawo Nijeriya.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa alƙalin ya bukaci a sanya ranar bayyanarsa daga makon 16 ga Maris, domin hakan zai ba shi da lauyansa damar halartar zaman.
Gayyar da hukumar CCB ta yi wa alkalin na da alaƙa da wani bincike da Premium Times ta gudanar, wanda ya yi zargin cewa alƙalin bai bayyana wasu asusun bankinsa ba a cikin takardar bayyana kadarori da ya gabatar a ranar 29 ga Afrilu, 2024.
Rahoton ya ce alkalin bai lissafa wasu asusun banki guda uku da ake zargin yana da su a UBA da kuma wani a Access Bank ba, duk da cewa dokar ƙasa ta wajabta wa jami’an gwamnati su bayyana dukkan kadarorinsu da asusun bankinsu.
Sai dai alƙalin ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa ya bi dukkan ƙa’idojin doka wajen bayyana kadarorinsa kamar yadda doka ta tanada.
