Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi
Shugaban kamfanin Golbokki ɓentures Limited, Alhaji Aminu Barau Liman Katagum, ya bayyana cewa kamfanin ya samu nasarar inganta fasahar noman doya da dankalin Hausa da na Turawa ba tare da amfani da takin zamani ba.
Alhaji Aminu Barau ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai a ofishinsa da ke unguwa masana’antu a kan hanyar Dumi a Bauchi, inda ya ce nasarar ta samu ne bayan dogon bincike da kamfanin ya gudanar domin bunkasa harkar noma a Nijeriya.
Ya ce kamfanin Golbokki ɓentures Limited na ci gaba da gudanar da bincike tare da hadin gwiwa da masana domin samar da hanyoyin da za su saukaka wa manoma aiki tare da kara yawan amfanin gona.
A cewarsa, sun shafe lokaci mai tsawo suna gudanar da bincike kan yadda za a bunkasa noman dankalin Hausa, dankalin Turawa da doya, wanda a yanzu ya kai wani mataki da zai taimaka wajen kara girman amfanin gona da kuma yawan abin da manomi zai samu a gonarsa.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu yana amfani da dankali da doyar da ya noma a gidansa, inda kuma ake sayar da su a kasuwa kuma jama’a na amfana da su.
Alhaji Aminu Barau ya bayyana cewa kamfanin na shirin fadada ayyukansa domin kara bunkasa harkar noma a matakai daban-daban kamar yadda ake yi a kasashen da suka ci gaba.
Ya kuma ce idan har gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi da hukumomin kula da aikin gona suka ba su goyon baya da tallafin da ya dace, kamfanin zai iya koyar da dubban manoma sabbin hanyoyin da suka gano domin bunkasa aikin gona a kasar nan.
A wani ɓangare kuma, shugaban kamfanin Golbokki ɓentures Limited ya bayyana cewa kamfanin ya samu gagarumar nasara a fannin noman shinkafa da ƙera injinan noma a Jihar Bauchi, musamman a yayin bikin cika shekaru 50 da kafuwar jihar.
Ya ce kamfanin ya shahara wajen noman shinkafa da zazzabarta, inda ake sarrafa shinkafar a cikin buhu na zamani irin yadda ake kawowa daga kasashen waje kamar Thailand, ba tare da samun datti ko kasa a cikinta ba.
Baya ga haka, ya ce kamfanin na kuma kera injinan noma da injinan zazzabar shinkafa, tare da samar da wasu kayayyakin da ake amfani da su wajen gudanar da ayyukan gona.
A cewarsa, kamfanin na kera injinan ne bisa la’akari da yanayin kasa da karfinta a Nijeriya da Afirka, domin yawancin injinan da ake shigowa da su daga kasashen waje kan lalace da wuri saboda ba su dace da yanayin kasar ba.
Ya bayyana cewa idan an shigo da wasu injinan daga kasashen waje, kamfanin na kan sake gyara su tare da canza wasu sassa domin su dace da yanayin gonaki da karfin kasa a Nijeriya.
A ƙarshe, Alhaji Aminu Barau Liman Katagum ya ce nasarar da kamfanin ke samu a ayyukansa ta samo asali ne daga baiwar da Allah Ya ba su da kuma haɗin gwiwar ƙwararrun ma’aikata da ke aiki a kamfanin.
