Daga RABIU SANUSI
Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya gargaɗi mambobin majalisar zartarwa ta Jihar da su guji rashin aminci ƙasa ta cikin gida da kuma fitar da bayanan sirrin gwamnati yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta ci gaba da lamuntar irin waɗannan halaye ba.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.
Gwamnan ya yi wannan gargaɗi ne yayin taron majalisar zartarwa karo na 38 inda ya buƙaci mambobin majalisar su kasance masu haɗin kai tare da sadaukar da kai ga manufofin gwamnatin domin ci gaban Jihar Kano.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa sabbin sauye-sauyen siyasa da suka faru a baya-bayan nan ne suka sa shi taro da muhimman masu ruwa da tsaki yanke shawarar daidaita tafiyarsu da jam’iyyar APC, domin inganta ci gaban jihar da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya.
Har ila yau, gwamnan ya tabbatar da cewa kwamishinoni biyar sun yi murabus sakamakon wannan sauyin siyasa inda ya ce huɗu daga cikinsu sun ajiye mukamansu bayan sun ƙi amincewa da komawa jam’iyyar APC.
Ma’aikatun da abin ya shafa sun haɗa da na harkokin jin ƙai, matasa tsaron cikin gida da kuma ayyuka na musamman.
Gwamna Yusuf ya amince da murabus ɗin nasu tare da yi musu fatan alheri a ƙoƙarin su na gaba.
Bugu da ƙari, gwamnan ya sanar da sauke shugaban ma’aikatan gwamnatin Jihar, Abdullahi Musa tare da tabbatar da naɗin Bilkisu Shehu Maimota a matsayin rikon ƙwarya na Shugabar ma’aikatan gwamnatin jihar, inda ya buƙace ta da ta inganta ladabi, haɗin kai da ƙwarewa a cikin aikin gwamnati na jihar.
