Da Ɗumi-Ɗumi An tabbatar da mutuwar sojojin Amurka huɗu bayan jirginta ya yi hatsari a Iraƙi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Huɗu daga cikin sojojin Amurka shida sun rasu a lokacin da jirgin ƙasar ya yi hatsari a yankin Yammacin Iraƙi, kamar yadda Cibiyar Tsaron Amurka (Centcom) ta bayyana.

Centcom ta ce ana cigaba da aikin ceto bayan ƙwacewar jirgin mai ƙirar KC-135, duk da cewa da farin ta ce bai kama da wuta ba a lokacin faruwa al’amarin.

Jirgin yana cikin waɗanda ke taimaka wa masu kai farmaki a yaƙin da ake cigaba gwabzawa tsakanin Amurka da Iran, kuma yana ɗaya daga cikin jirage biyu da iftila’in ya afka wa.

A cewar Centcom, al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na daren Alhamis wayewar Juma’a, inda har zuwa yanzu ana cigaba da gudanar da bincike akan gano musabbabin faruwar al’amarin.

Aƙalla sojojin Amurka bakwai suka rasu tun bayan fara yaƙin da aka yi tsakanin tsakaninta da ƙawarta a gefe guda da kuma Iran a ɗaya ɓangaren.

Haka kuma, wannan ya nuna cewa rundunar sojin Amurka ta rasa jiragen sama huɗu yayin da ake cigaba da fafatawa.

By Babaji