
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Aƙalla sanatoci guda tara daga jam’iyyu uku sun sanar da Majalisar Dattawa cewa sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar adawa, ADC.
Sanatocin da suka fice jam’iyyar LP sun haɗa da Victor Umeh, Tony Nwoye da Ireti Kingibe.
Sauran biyar kuwa, sun fice ne daga PDP waɗanda sune: Aminu Waziri Tambuwal, Binos Yaroe, Lawal Adamu Usman, Mohammed Ogoshi Onawo da Augustine Akobundu.
Haka kuma Enyinnaya Abaribe daga APGA shi ma ya koma ADC, sai dai Majalisar Dattawa ta ba shi wa’adin mako guda ya sake nazarin matakin, tana mai cewa hujjar da ya bayar ta ficewa daga jam’iyyarsa ba ta cika sharuddan kundin tsarin mulki ba.
Hakan na nufin an samu kujeru uku daga Nasarawa ta Arewa, Enugu ta Arewa, da kuma daga Ribas ta Kudu maso Gabas, da aka samu sakamakon rasuwar sanatocin.
Bayan wannan, jam’iyya mai mulki, APC tana da guda 87, ADC 9, PDP 6, Accord 1, APGA 1, NDC 1 da kuma NNPP mai guda 1.
