Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
ƙaruwar sauya sheƙa da yake girgiza jam’iyyar PDP gabanin babban zaɓen shekarar 2027 ya sake bayyana a Majalisar Dattawan Nijeriya, inda wasu sanatoci uku suka fice daga jam’iyyar suka koma jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar.
Sanatocin da suka sauya sheƙa sun haɗa da Amos Yunana mai wakiltar Adamawa ta Arewa, Aminu Iya Abbas mai wakiltar Adamawa ta Tsakiya da kuma Ikra Aliyu Bilbis mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya. An karanta wasiƙun sauya jam’iyyarsu ne a zaman majalisa na ranar Laraba.
Sauya sheƙar sanatocin guda uku ya zo ne kwana guda bayan da Sanata Banigo Ipalibo, mai wakiltar Ribas ta Yamma, ita ma ta bar PDP ta koma APC a ranar Talata. Wannan sauyin ya rage yawan sanatocin PDP a majalisar daga 17 zuwa 14, yayin da adadin sanatocin APC ya ƙaru daga 81 zuwa 84.
Da yake martani bayan sauyin, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa abin da ke faruwa a yanzu a majalisar abu ne da ba a taɓa ganin irinsa ba tun bayan samun ’yancin kai a Nijeriya a shekarar 1960.
Akpabio ya yi wannan bayani ne bayan da aka sauya kujerun sabbin sanatocin daga ɓangaren jam’iyyar adawa zuwa gefen jam’iyyar APC a zauren majalisar.
Ya ce, sauya sheƙar sanatocin PDP zuwa APC a yanzu na kama da daidaito idan aka kwatanta da abin da ya faru a shekarar 2018 a Majalisa ta Takwas, lokacin da sanatoci da dama suka bar APC suka koma PDP, ciki har da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki.
A cewarsa, a wancan lokaci kusan sanatoci 30 ne suka sauya jam’iyya daga APC zuwa PDP a rana guda, yayin da a yanzu kuma akasin haka ke faruwa a Majalisa ta Goma, inda sanatocin PDP ke komawa APC saboda abin da ya kira kyakkyawan shugabanci da manufofin gyara tattalin arziki da gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa.
Tun da farko, Jagoran Majalisar Dattawa, Sanata Micheal Opeyemi Bamidele, mai wakiltar Ekiti ta Tsakiya, ya ce yawan sanatocin da ke barin PDP da sauran ƙananan jam’iyyu suna komawa APC alama ce da ke nuna cewa tsarin mulki da tafiyar ƙasa na tafiya daidai a ƙarƙashin shugabancin Shugaba Tinubu.
