Ministan Tsaro ya gargaɗi kafafen yaɗa labarai kan yaɗa farfagandar ’yan ta’adda

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA, Abuja

Ministan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, ya buƙaci kafafen yadlɗa labarai a faɗin ƙasar nan da su riƙa nuna ƙwarewa da tsantsar gaskiya a rahotanninsu, tare da kauce wa yaɗa farfagandar ’yan ta’adda da ka iya raunana gwiwar sojoji ko ba wa masu aikata laifi ƙwarin gwiwa.

Musa ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake ganawa da manema labarai bayan wata muhimmiyar ganawa da shugabannin rundunonin sojin ƙasar domin duba yadda ake gudanar da ayyukan tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.

Taron ya haɗa da Babban Hafsan Tsaro da shugabannin rundunonin sojojin ƙasa, ruwa da sama, inda suka yi nazari kan dabarun da ake amfani da su wajen yaƙi da ta’addanci, fashi da makami da sauran barazanar tsaro da ke addabar ƙasar.

A cewar ministan, rahotanni masu inganci da alhakin aikin jarida na taka muhimmiyar rawa wajen ƙara ƙarfin gwiwar sojoji da ke fafatawa da ’yan ta’adda a fagen daga.

Ya yi gargadin cewa yaɗa bayanan da ba a tantance ba ko kuma saƙonnin da ƙungiyoyin ta’addanci ke yaɗawa na iya gurgunta kokarin sojoji tare da rikita fahimtar jama’a kan halin da tsaro ke ciki a ƙasar.

Duk da amincewa da cewa rundunar sojin ƙasar ta yi asarar wasu jami’ai yayin gudanar da ayyukan tsaro, Musa ya jaddada cewa sojoji na ci gaba da yi wa ’yan ta’adda da ’yan bindiga mummunar illa ta hanyar farmakin da suke kaiwa.

Ya ce, “Rundunar tsaro na ci gaba da yi wa ’yan ta’adda da ’yan bindiga babbar illa, ciki har da kashe wasu daga cikin manyan shugabanninsu tare da lalata sansanoninsu da kayan aikinsu.”

Ministan ya sake jaddada kudirin rundunar sojojin kasar, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, na ƙara tsaurara ayyukan soja domin rusa cibiyoyin ’yan ta’adda da dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar.

Haka kuma ya buƙaci ’yan Nijeriya da su riƙa bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai da za su taimaka wajen gudanar da ayyukan yaƙi da masu aikata laifi.

A cewarsa, magance matsalar tsaro na bukatar haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro da kuma al’umma baki ɗaya.

Ministan ya gargaɗi cewa duk wanda aka samu yana taimakawa kungiyoyin ta’addanci ta hanyar bayanai, kayan aiki ko wata gudummawa, za a ɗauke shi a matsayin abokin laifi kuma za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.

Ya kuma tabbatar da cewa karkashin jagorancin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnatin tarayya na ci gaba da ba wa rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro dukkan goyon bayan da suke bukata domin kare lafiyar kasa.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Babban Sakataren Ma’aikatar Tsaro Richard Pheelangwah, Babban Hafsan Tsaro Janar Olufemi Oloyede, Babban Hafsan Sojin Kasa Laftanar Janar Waidi Shuaibu, Babban Hafsan Sojin Ruwa ɓice Admiral Idi Abbas, Babban Hafsan Sojin Sama Air Marshal Sunday Aneke, da kuma Babban Hafsan Sashen Leƙen Asirin Soji Laftanar Janar Emmanuel Udieandeye.

By ukarofi