Majalisar Birtaniya ta rusa tsarin kujerun gado na sarakuna a majalisar dattijai 

Spread the love

Majalisar dokokin ƙasar Birtaniya ta amince da wata sabuwar doka da za ta kawo ƙarshen tsohon tsarin da ke bai wa wasu ‘yan aristocrats damar zama mambobin Majalisar Dattijai saboda gadon sarauta kawai.

Sabuwar dokar, wadda aka fi sani da Hereditary Peers Bill, ta samu amincewa a daren Talata a Majalisar Dattijai ta ƙasar, lamarin da ya kawo ƙarshen wani tsarin siyasa da ya shafe ƙarni da dama yana aiki a Birtaniya.

Wannan mataki wani muhimmin ɓangare ne na shirin gyaran majalisar da gwamnatin Firaminista Keir Starmer ta jam’iyyar Labour ta ɗauka domin sabunta tsarin majalisar dokokin ƙasar.

A cikin tsarin da aka soke, wasu mutane daga gidajen sarauta ko manyan iyalai na aristocrats na iya zama mambobin Majalisar Dattijai saboda gadon sarauta da suka samu daga iyayensu, ba tare da wani zaɓe ko nadin gwamnati ba.

Sai dai shugabar Majalisar Dattijai ta Birtaniya, Angela Smith, ta bayyana cewa tsarin bai dace da tsarin dimokuradiyya na zamani ba.

Ta ce, “Majalisar Dattijai na taka muhimmiyar rawa a tsarin majalisa mai ɓangarori biyu na ƙasar nan, amma bai kamata mutum ya samu kujera saboda gadon sarauta kawai ba.”

Ta ƙara da cewa amincewa da wannan doka shi ne mataki na farko na manyan gyare-gyare da gwamnati ke shirin yi a majalisar.

Asalin wannan gyara ya samo asali ne tun a shekarar 1999 lokacin da tsohon Firaministan Birtaniya Tony Blair ya fara rage yawan mambobin majalisar da ke samun kujeru ta gadon sarauta.

A wancan lokaci, fiye da mutane 600 daga irin waɗannan ‘yan aristocrats aka cire daga majalisar.

Sai dai an bar 92 daga cikinsu a matsayin wani matakin wucin gadi domin sauƙaƙa sauyin tsarin. Yanzu kuma sabuwar dokar ta kawo ƙarshen wannan tsarin gaba ɗaya.

Majalisar Dattijai ta Birtaniya tana zaune ne a cikin tsohon ginin Palace of Westminster a birnin Landan.

Majalisar na da kusan mambobi 800, yawancinsu ana nadinsu ne a matsayin mambobi na rayuwa ta hanyar shawarar Firaminista ko wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Haka kuma akwai wasu bishof-bishof na Cocin Ingila da ke zama a majalisar. Sai dai masu sukar tsarin sun daɗe suna cewa tsarin nadin mambobin yana da matsaloli, musamman batun son kai da kuma girman majalisar da ya zarce na wasu majalisun duniya.

A tsarin siyasar Birtaniya, Majalisar Dattijai na iya gyara dokoki da Majalisar Wakilai ta ƙasa ta gabatar. Sai dai ba ta da ikon dakatar da dokar gaba ɗaya, domin Majalisar Wakilai, wadda ake zaɓar mambobinta, na iya soke duk wani gyara da majalisar dattijai ta yi. Saboda haka ana kallon wannan mataki a matsayin wani muhimmin sauyi da zai iya sake fasalin tsarin siyasar Birtaniya a nan gaba.

By ukarofi