
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani jirgin ƙasa da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Tarayya Abuja, ya yi hatsari a safiyar yau Litinin, lamarin da ya jikkata mutane da dama da haddasa tsaiko ga zirga-zirga.
Rahotanni sun bayan cewa al’amarin ya faru ne bayan an ƙara wani tarago ga jirgin a yankin Jere da ke Jihar Kaduna kafin tafiyar ta yi nisa.
Wasu daga cikin fasinjojin da lamarin ya rutsa da su sun ce jirgin ya taso ne daga Kaduna da misalin ƙarfe 7:15 na safe, amma taragon da aka ƙara ya kwance daga baya, lamarin da ya haddasa hatsarin duk da cewa an ɗauki tsawon lokaci kafin a gyara jirgin domin cigaba da tafiyar.
Shaidun gani da ido sun ce fasinjoji da dama sun shiga cikin firgici da gajiya sakamakon tsoron abin da ya faru.
A lokuta da dama ana samun irin waɗannan haɗurran akan hanyar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, wadda dubban matafiya ke amfani da ita a kullum domin samun sauƙin zirga-zirga.
