Sarki ya sayi jirgi mara matuƙi da ɗaukar jami’ai 118 kan rashin tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Laraba Sarkin Masarautar Okpella a Jihar Edo da ke Kudancin Nijeriya, wato Mai Martaba Mike Sado, ya sayi jirgi mara matuƙi da ɗaukar jami’an tsaro a da guda 100 domin magance matsalar rashin tsaro a Ƙaramar Hukumar Estako da kewayenta.

Ya kuma ce zai samar da gina babban ofishi ga jami’an ‘yan sandan yankin domin inganta lamuran tsaro a yankin.

Sarkin ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai, inda ya yi watsi da rahoton da ke cewa Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta kama shi.

Ya ce, wasu daga cikin na ƙasa da shi da suka saba raba kuɗaɗen ci-gaban yankin a tsakaninsu sun nuna rashin jin daɗi game da gyare-gyaren da ya samar da tsawon watanni bakwai da suka gabata.

Daga ciki, ya tabbatar da toshe ƙofar sarrafa kuɗaɗen yankin ta hanyoyin da ba su dace ba, inda ya ƙara da cewa an ga ci-gaba a fannin ababen more rayuwa tun hawansa karagar mulkin.

Kazalika, ya ce zargin ƙorafin EFCC da aka jingina masa an yi ne don kawai a ɓata masa suna saboda ya hana raba kuɗaɗe tsakanin wasu tsiraru wajen yin amfani da su wajen gina yankin.

A cewarsa, ya ƙara adadin kuɗin shiga da ake samu daga N120,000 zuwa sama da miliyan N8.

By Babaji