Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Sarauniyar Hausawan Afirka, Amb. Dakta Hajiya Umaimatu Muhammad, wacce aka fi sani da Uwar Marayu, ta bayyana cewa a cikin watan Disamba da ya gabata kaɗai ta aurar da marayu guda 24, a wani ɓangare na ƙoƙarinta na tallafa wa marasa galihu a cikin al’umma.
Ta bayyana hakan ne yayin da take jawabi kan yadda ake inganta rayuwar marayu da masu ƙaramin ƙarfi, inda ta ce har yanzu ba ta da ƙididdigar adadin marayun da take tallafawa, amma tana ci gaba da taimaka musu gwargwadon iko.
A cewarta, “Wannan hidima ta marayu tana ba ni matuƙar farin ciki da jin daɗi. Duk lokacin da na haɗu da maraya ko marainiya, ina ƙoƙarin taimaka masa ko ita da abin da Allah Ya hore mini.”
Sarauniyar ta ƙara da cewa ita ma ta taso a matsayin marainiya, amma ta samu kulawa daga ‘yan’uwan mahaifinta wanda hakan ya sa ba ta fuskanci tsananin wahala ba. Sai dai ta ce hakan ne ya ƙara sanya mata tausayi ga marayu, wanda ya zama ginshiƙin ayyukanta na jin ƙai.
Ta kuma bayyana cewa tana tabbatar da cewa duk marainiyar da ta aurar ana tanadar mata da kayan ɗaki masu inganci, ciki har da gadaje da sauran kayayyakin more rayuwa, domin fara rayuwar aure cikin kwanciyar hankali.
Bugu da ƙari, ta ce tana da wata makarantar Islamiyya da ke ƙarƙashin jagorancin Malam Hafizu Abubakar, wacce ke ɗauke da ɗalibai da dama, musamman marayu, domin ba su ilimi da tarbiyya.
Sai dai ta nuna cewa duk da irin ayyukan da take yi, ba ta samun wata gudummawa daga hukumomi ko ƙungiyoyi, inda ta jaddada cewa a shirye take ta yi aiki tare da duk wata hukuma ko ƙungiya mai son taimakawa wajen kula da marayu.
